Mai baiwa Gwamnan Kano shawara ya fice daga Jam’iyyar NNPP

Date:

 

 

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya karɓi mai baiwa Gwamnan Jihar Kano shawara, Alhaji Sani Abdulkadir Dambo, zuwa jam’iyyar APC daga jam’iyyar NNPP.

Dambo, wanda ya taɓa riƙe shugabancin Hukumar Tara Haraji ta Jihar Kano sau biyu, ya sanar da ficewarsa daga NNPP zuwa APC, yayin ziyarar da ya kai wa Sanata Barau a gidansa da ke Abuja a ranar Litinin.

A ranar 13 ga watan Agusta, an naɗa Dambo a matsayin mai bai wa Gwamnan Kano Shawara na Musamman kan Zuba Jari, inda Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya sa hannu kansa a takardar naɗin nasa.

Farashin Mai: Takaddama ta barke tsakanin Ɗangote da NNPC

Yayin sanar da ficewarsa daga NNPP, Dambo ya yi alƙawarin yin aiki tare da jam’iyyar APC a Kano da kuma matakin ƙasa baki ɗaya.

“Na gode wa Allah Maɗaukakin Sarki da ya shiryar da ni, ya kuma ba ni ikon dawowa gida. Na kasance a cikin wannan gida kafin na koma NNPP, amma yanzu na dawo APC.

“Za mu ci gaba da tallafa wa wannan tafiya tare da ƙoƙarinmu na kasancewa masu biyayya ga APC a Kano da kuma matakin ƙasa baki ɗaya.

“Zan yi amfani da dukkanin basirata da ƙwarewata wajen tallafa wa nasarar APC. Ina fatan Sanata Barau zai samu nasara. Kazalika, ina miƙa gaisuwata ga Shugaban APC na Ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje. Allah ya ci gaba da masa jagoranci,” in ji Dambo.

Maulidi: Minista T Gwarzo ya bukaci al’ummar Musulmi su rika koyi da halayen Annabi S A W

Har wa yau, ɗaya daga cikin manyan jagororin NNPP a ƙaramar hukumar Kabo a Jihar Kano, Alhaji Rabiu Alhassan Durum, ya koma jam’iyyar APC.

Yayin da yake maraba da ’yan siyasar biyu zuwa jam’iyyar APC, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa ya yaba musu bisa wannan hukunci da suka yanke.

Sanata Barau, wanda kuma shi ne Mataimakin Kakakin ƙungiyar ECOWAS, ya sake jaddada aniyar Gwamnatin Tarayya da jam’iyyar APC ke jagoranta na magance ƙalubalen da ƙasar nan ke fuskanta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi: Tinubu ya Iso Kano domin ta’aziyyar Dantata

Shugaban Nigeria Bola Ahmad Tinubu ya iso jihar Kano...

ALGON ta Kano Sa’adatu Soja ta sami sabon matsayi a kungiyar ALGON ta Ƙasa

Daga: Aliyu Danbala Gwarzo. Shugabar karamar hukumar Tudunwada kuma ALGON...

Da dumi-dumi: Tinubu zai zo Kano

Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu zai zo Kano ranar...

Tinubu ya sauya sunan jami’ar Maiduguri zuwa Sunan Muhd Buhari

Shugaba Bola Tinubu ya sauya sunan Jami'ar Maiduguri zuwa...