Hauhawar farashi ya ragu zuwa kashi 32.15 – NBS

Date:

Duk da hauhawar farashin kayayyaki da ake fama da shi a faɗin Najeriya, Hukumar Kididdiga ta Ƙasa (NBS), ta sanar da cewa hauhawar ta ragu zuwa kashi 32.15 a watan Agusta da kuma kashi 33.40 a watan Yuli, 2024.

Wannan yana nuna cewa hauhawar farashi ta ragu da kashi 1.25 a watan Agusta, duk da tsadar abincin da ake fama da ita a ƙasar.

Majalisar Wakilan Nigeria ta sha alwashi hukunta duk masu hannu a cin zarafin sojan nan Seaman Abbas

Sai dai idan aka kwatanta da watan Agusta 2023, hauhawar farashi ta ƙaru da kashi 6.35, domin a wancan lokacin farashin yana kashi 25.80.

NBS ta bayyana cewa, “Wannan yana nuna cewa hauhawar farashi ta ƙaru a watan Agusta 2024, idan aka kwatanta da watan Agusta 2023.”

Farashin Mai: Takaddama ta barke tsakanin Ɗangote da NNPC

Hauhawar farashi a watan Agustan 2024 ta kasance kashi 2.22, inda ya ragu da kashi 2.28 a watan Yuli 2024.

A taƙaice, wannan ya nuna an samu ƙarin farashin kayayyaki kaɗan a watan Agustan 2024, idan aka kwatanta da watan Yuli 2024.

Ko da yake tsadar rayuwa na ci gaba da tasiri, sakamakon ƙarin farashin man fetur da aka samu sama da kashi 354.

Daily trust

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin Sarautar Kano: Fadar Sarki Sanusi ta zargi magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero da kai farmaki Kofar Kudu

Daga Sani Idris Maiwaya   Rikicin Masarautar kano ya na neman...

Shugabannin Kasuwar Kanti Kwari sun shiryawa Gwamnan Kano Addu’o’i na musamman

Daga jafar adam Shugaban kasuwar Kantin Kwari Sharu Abdullahi Namalam...

Dalilin Kwankwaso na kin shiga Hadakar ADC

Jam'iyyar NNPP ta ce abin da ya sa ba...