Farashin Mai: Takaddama ta barke tsakanin Ɗangote da NNPC

Date:

Daga Maryam Muhammad Ibrahim

 

Kamfanin Ɗangote ya musanta labarin da mai magana da yawun kamfanin mai na ƙasa NNPC Kan farashin da suka sayi man fetur din da matatar Ɗangote ta tace.

Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito mai magana da yawun kamfanin NNPC Olufemi Soneye ya ce sun fara sayan man na matatar Ɗangote akan Naira 898 kowacce lita.

A cikin wata sanarwa da shugaban sashin hulda da jama’a na kanfanin Ɗangote Anthony Chiejina ya sanyawa hannu kuma aka rabawa manema labarin, kamfanin ya ce jawabin na mai magana da yawun NNPCL ba gaskiya ba ne.

NNPC ya fitar da farashin da yan Nigeria za su rika sayan man fetur din Ɗangote

” Muna kira ga yan Nigeria da su yi watsi da waccan maganar domin an yi ta ne da gangan don a bata sunan kamfanin Ɗangote, wanda ya kai kusan Shekaru 50 ya na samawa yan Nigeria sauki a harkokin kasuwancinsa”.

” Ku jira karamin kwamitin saya da sayar da man fetur din da kudin Nigeria wato Naira wanda shugaban kasa Bola Tinubu ya kafa ya Fara aiki a ranar 1 ga watan October mai zuwa.

Ɗangote ya ce ya kamata yan Nigeria su sani man fetur din da aka fara fitar da shi a yau Lahadi 15 ga watan Satumba sun Sayo shi ne da Dala ba da Naira ba, kuma mu ma mun sayarwa da NNPCn man ne da Dala ba Naira ba, amma fa mun yi musu sauki ba kamar yadda suke sayo a kasashen waje ba.

Sanarwar ta ce Kamfanin Ɗangote ya na baiwa yan Nigeria tabbatacin wadata kasar da man fetur domin magance karancinsa a fadin ƙasar.

Sai dai shi ma Kamfani na NNPC ya tabbatar da cewa da dala ya sayi man ba da Naira ba, Inda ya ce zai fara sayan man da Naira ne daga ranar 1 ga watan October mai zuwa.

A cikin wata sanarwa da Kamfanin na NNPC ya fitar da safen nan ya bayyana farashin da za a sayar da man Ɗangote a kowacce jiha a Nigeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Iftila’i: An tsinci gawar wata dattijuwa mai shekaru 96 cikin rami masai a Kano

A ranar Alhamis al’ummar ƙauyen Sarai da ke ƙaramar...

Na riga Kwankwaso shiga harkokin Siyasa – Sanata Barau Jibrin

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya...

Jaridun Amurka sun bankado Tsare-tsare uku da sojojin Amurka ke yi don tunkarar Najeriya

Rahotanni daga wasu jaridun Amurka na bayyana cewa rundunar...

Dalibai 22 sun kammala karatu da daraja ta 1 a bikin yaye ɗalibai na farko na Jami’ar Baba-Ahmed Kano

Jami’ar Baba-Ahmed, Kano ta gudanar da bikin yaye ɗalibai...