Kamfanin man fetur na Najeriya (NNPCL) ya bayyana cewa ya sayi man fetur a kan Naira 898 kan kowace lita daga matatar Dangote.
Kamfanin mai ya kai kwashe kimanin manyan motoci 300 zuwa matatar mai da ke Legas, ranar Asabar, kuma an fara lodin a ranar Lahadi.
YANZU-YANZU: Obasanjo Ya Isa Minna, Domin Gana wa da IBB, Abdulsalami, Gusau
Da yake zantawa da daily trust kan farashin man fetur din, Kakakin Hukumar NNPC, Olufemi Soneye, ya ce, “Mun yi nasarar fara lodin man fetur a matatar Dangote a yau. Batun cewa mun sayi man fetur din akan Naira 760 a kowace lita ba gaskiya ba ne. Wannan lodin na farko, daga matatar Ɗangote sun sayi kowacce lita akan Naira 898 ne.”
Ya shaida wa daily trust cewa, ya zuwa lokacin hada wannan rahoton an yi lodin manyan motoci sama da 70.