Daga Rukayya Abdullahi Maida
Sababbin Shugabannin Kungiyar yan jaridu ta kasa reshen jihar Kano sun kai ziyarar inganta alaka da rundunar yan sandan jihar kano.
Da yake bayyana makasudin ziyarar shugaban kungiyar yan jaridu ta kasa reshen jihar Kano Kwamared Sulaiman Abdullahi Dederi Wanda ya samu wakilcin mataimakin sa Kwamared Mustapha Gambo Mohd ya ce sun kai ziyarar ne domin kara kulla alakar aiki tsakanin yan jaridu da Rundunar yan sanda a Kano.
Comrade Sulaiman Dederi wanda ya bayyana muhimmancin hadi gwiwa domin yin aiki tare da dukkanin bangarorin biyu domin cigaban al’umma da tabbatar da tsaron rayuka da dukiya, ya kuma nemi hadin kai da goyon rundunar domin gudanar da aikinsu cikin nasara.
Shugaban kungiyar yan jaridun na Kano ya nuna gamsuwarsa bisa hadin kai da Kwamishinan yan sandan ke baiwa yan jarida a Kano.
A nasa jawabin Kwamishinan yan sanda na jahar kano Alh. Salman Dogo Garba ya yi alkawarin rubanya alakar aiki da Yan jarida tare da sauraron shawarwari daga kungiyar yan jaridu tare da mutunta aikinsu.
Ya kuma ba da tabbacin baiwa kungiyar cikakken hadin kai da goyon baya domin gudanar da aikinsu yanda ya kamata, sannan ya yiwa sababbin shugabanin fatan alkhairi.
Kwamishinan yace kofarsa a bude ta ke ga Yan jarida a kowane lokaci.