Yadda ambaliyar ruwa ta mamaye gidaje a Maiduguri

Date:

Dubban mutane sun bar gidajensu sakamakon gagarumar ambaliya a garin Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Da talatainin dare ne ambaliyar ta mamaye Fadar Shehun Borno da tituna da gidaje da gadojin da sauran wurare, lamarin da ya tilasta wa jama’a sauya matsuguni.

Wasu majiyoyi sun ce an shekara kimanin 30 rabon da a ga irin wannan albaliya a garin Maiduguri.

Yan sanda a Kano sun kama matashin da aka hada baki da shi aka sace dan yayansa mai Shekaru 4

Wani shaida ya bayyana cewa a daren ne Madatsar Ruwa ta Alao Dam da ke kusa da garin Maiduguri ta fashe.

Ya ce ruwan ambaliyar ya yi ƙarfin gaske inda ya mamaye Fadar Shehun Borno, Kofa Biyu, Gadar Fori wadda ta haɗa Fori da Galtimari zuwa Tashan Bama.

A cewarsa, unguwannin da lamarin ya fi ƙamari sun haɗa da Fori, Galtimari, Gwange, da Bulabulin.

“Kowa ya kaurace wa yankin post office, kasuwar Monday Market zuwa zoo da gidan man Hissan saboda ambaliya ta riga ta shanye su, mota ba ya iya bi,” in ji Refeal.

Rabon Tallafi a Kano: Kwankwaso ya koka wa shugaba Tinubu

“Da mislain 12:30 aka sanar da mu cewa mu kwashe ’yan kananan kayan da za mu iya, amma kafin mu ciro takardun shaidar karatumu, har ruwan ya kawo mana mara,’ in ji wani mazaunin Galtimari.

Bilyaminu Yusuf, ya ce, “muna cikin mawuyacin hali a Lagos Street, ambaliya ta sa mu hijira zuwa makarantar Firamare ta Galtimari mun bar kayanmu a gida.”

Wakilin daily trust ya gano yadda ruwan ya shanye Gadar Lagos Street, daya daga cikin manyan gadojin da ke garin Maiduguri.

Hakazalika gidan radiyo da talabijin na jihar (BRTV) Post Office, Shehu Laminu way, da unguwar Custom su ma ambaliyar ta shafe su.

Wani ma’aikacin BRTV ya wallafa a Soshiyal Midiya cewa, “ruwa ya shanye ofishinmu da Post Office.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...