Masana: Amfanin masara a jikin Ɗan Adam

Date:

Daga Zubaida Abubakar Ahmad

Masana kiwon lafiya a fannin ingantacen abinci wato dietians ko nutritions sun tabbatar da cewa Masara na daya daga cikin amfanin gona mai gina jiki.

Masara ta ƙunshi sinadarai da sauran bitamin da ma’adanai. Sannan tana cikin hatsi mara tsada kuma mai sauƙin samuwa, kuma masara na ƙunshe da sinadarai da yawa irin su carbohydrates wato abincin mai kara karfin jiki da furotin wato abincin da yake kara inganta lafiyar jiki da jiba ma kyau. fiye da yadda ake zato.

Masara na rage haɗarin kamuwa da ciwon sukari nau’i na biyu, kuma za ta iya taimakawa wajen hana mutum kamuwa da sankarar hanji. Tana kuma ƙara lafiyar zuciya.

Rabon Tallafi a Kano: Kwankwaso ya koka wa shugaba Tinubu

Masara na ƙunshe da sinadirin Folic acid dake taimakawa jiki wajen yaƙar tarin majina, kuma dusarta wato (fiber) tana kara wa ciki lafiya, wanda hausawa kicewa baka lafiya ciki lafiya kuma tana sauke jinin dake yawan hauhawa.

Iftila’i: Yadda muggan dabbobi suka shiga cikin al’umma a maiduguri sakamakon ambaliyar ruwa

Masara tana karawa idanu lafiya da haske domin ta na kunshe da sinadirin vitamin A da ya ninka na sauran abinci har sau goma.

Tana karfafa garkuwar jiki ta yadda za a samu kariya daga barazanar wasu cututtuka.

A saboda haka ne masana suke ba da shawarar amfani da masara domin amfana daga gareta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Abubakar Bichi ya bada gudumawar motocin bas 13 ga jami’o’in Kano da taraktoci 11 ga yan mazabarsa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu Dan Majalisar tarayya mai wakiltar karamar...

Rikicin Sarautar Kano: Fadar Sarki Sanusi ta zargi magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero da kai farmaki Kofar Kudu

Daga Sani Idris Maiwaya   Rikicin Masarautar kano ya na neman...

Shugabannin Kasuwar Kanti Kwari sun shiryawa Gwamnan Kano Addu’o’i na musamman

Daga jafar adam Shugaban kasuwar Kantin Kwari Sharu Abdullahi Namalam...