Karin kudin mai: Gwamnan Legos ya sassautawa ma’aikatan jihar

Date:

Daga Maryam Muhammad Ibrahim

 

Gwamnatin jihar Legas ta baiwa ma’aikatan jihar damar su rika gudanar da aiki daga gidan har na tsahon watanni uku sakamakon karin farashin man fetur da aka yi a Nigeria.

Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya amince da hakan a wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban ma’aikatan jihar Mista Bode Agoro a ranar Laraba.

Yan arewa ku yi mana aikin gafara, mun gaza kare ku – ACF

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya ya ba da rahoton cewa, a ranar 28 ga Fabrairu, gwamnan ya ba da umarnin cewa ma’aikatan za su yi aiki daga gida na wasu kwanaki.

Wannan Sabon matakin da gwamnatin jihar Lagos ta dauka ya nuna cewa ta sake tsawaita tsarin nata don saukakawa ma’aikatan gwamnatin jihar.

Ya ba da umarnin cewa ma’aikatan da suke matakin Albashin na 01 zuwa 14 an ba su damar yin aiki daga gida na kwana biyu a cikin kowanne mako, yayin da su kuma waɗanda su ke matakin Albashin na 15 zuwa 17 aka ba su damar yin aiki daga gida na kwana ɗaya a cikin mako.

Kotu ta tusa keyar alƙalin bogi zuwa gidan yari a Kano

An yanke shawarar ne don rage tasirin cire tallafin man fetur ga ma’aikata.

Sanwo-Olu ya bayyana cewa tsarin zai saukakawa mafi yawa daga cikin ma’aikata, kuma tsarin dama ce ga dukkanin masu aiki a ma’aikatu da hukumomin gwamnatin jihar daban-daban.

NAN ta ruwaito cewa karin wa’adin ya fara aiki ne daga ranar 4 ga watan satumba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi: Tinubu ya Iso Kano domin ta’aziyyar Dantata

Shugaban Nigeria Bola Ahmad Tinubu ya iso jihar Kano...

ALGON ta Kano Sa’adatu Soja ta sami sabon matsayi a kungiyar ALGON ta Ƙasa

Daga: Aliyu Danbala Gwarzo. Shugabar karamar hukumar Tudunwada kuma ALGON...

Da dumi-dumi: Tinubu zai zo Kano

Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu zai zo Kano ranar...

Tinubu ya sauya sunan jami’ar Maiduguri zuwa Sunan Muhd Buhari

Shugaba Bola Tinubu ya sauya sunan Jami'ar Maiduguri zuwa...