Dalilin da yasa gwamnan Kano ya kwace kwangilar Titin Garko mai tsawon kilomi biyar

Date:

Daga Kamal Yahaya Zakaria

 

Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya ziyarci Dam din Kafinchiri a karamar hukumar Garko, domin ganin yadda aiki ke gudana, wanda aka bayar da shi a yunkurin kawo sauyi a fannin noma a jihar.

Aikin, wanda darajarsa ta kai Naira biliyan 2.5, an yi shi ne da nufin bunkasa noman rani da damina, da inganta samar da abinci, da kuma bunkasa tattalin arzikin jihar.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya aikowa kadaura24 a ranar Lahadi.

Shahararren mawakin siyasa ya rasu a Kano

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya jaddada muhimmancin aikin noman na Kafinchiri, inda ya bayyana hakan a matsayin wani muhimmin bangare na kokarin gwamnatinsa na bunkasa noma a jihar Kano.

Ya bukaci mazauna garin Garko da kewaye da su yi amfani da damar da aikin zai bayar domin inganta tattalin arzikin su da jihar baki daya.

Talla
Talla

A wani labarin kuma, Gwamnan ya sanar da kwace kwangilar aikin hanyar karamar hukumar Garko mai tsawon kilomita biyar saboda gazawar dan kwangilar na dawowa bakin aiki .

Ya ba da tabbacin cewa nan ba da jimawa ba za a baiwa wani mai kwazo kwangilar aikin don tabbatar da kammala aikin a kan kari.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kuma kuduri aniyar samar da cibiyar lafiya ta zamani a garin Garko, da nufin kusantar da harkokin kiwon lafiya ga jama’a.

Ya nuna jin dadinsa bisa goyon bayan da al’ummar yankin suke ba shi tare da jaddada aniyar gwamnatinsa na ci gaba gudanar da aiyukan cigaba a jihar .

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bayan tura Kashim ya taho da gawar Buhari, Tinubu ya ba da umarnin sassauta Tutar Nigeria

Shugaban kasa Bola Tinubu ya bada umarnin ayi kasa...

Yanzu:yanzu: Tsohon shugaban Nigeria Buhari ya rasu

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un!!! Allah yayi wa tsohon shugaban...

Tinubu ka fadawa yan Nigeria Inda ka tsaya har kwana 5 bayan taron BRICS – ADC

    Jam'iyyar African Democratic Congress wato ADC ta soki Shugaban...

Da dumi-dumi: Yadda akai Jami’an tsaro suka kama ni -Danbello

Rahotannin sun tabbatar da cewa jami'an tsaro a Nigeria...