Allah Ya yi wa shahararren mawakin siyasar nan, Alhaji Garba Gashuwa rasuwa.
Ƴar marigayin, Maryam Garba Gashuwa ta shaida wa wakilin BizPoint Hausa cewa mahaifin na su ya rasu yau da asuba a Asibitin Kwararru na Murtala da ke Kano.
Ta ce ya rasu bayan ya sha fama da jiyya.
A cewar ta, marigayi Gashuwa ya haura shekara 70 kafin rasuwar ta sa.
Ya rasu ya bar ƴaƴa 11, mata biyu da kuma jikoki da dama.
