Masu larurar ido 3,000 ne suka amfana da aikin ido kyauta a kananan hukumomin kura madobi da garin malam

Date:

Daga Aliyu Danbala Gwarzo

 

Dan majalissar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin kura madobi da garin malam Hon. Yusuf umar Datti ya kaddamar da aikin ido tare da bada magunguna kyauta ga masu fama da Larurar ido a yankin.

Taron kaddamarwar ya gudana ne a asibitocin kura da madobi da garin malam a ranar Juma’a wanda itace ranar da aka fara gudanar da aikin wanda zai dauki kwanaki 3 ana gudanarwa.

Da yake jawabi a yayin kaddamarwar Yusuf Datti kura yace ya bijiro da shirin kula da lafiyar masu Lalurar idanu ne saboda muhimmancin da ido Ke da shi a rayuwar al’umma.

“Lafiyar ido ita ce ginshiki matukar mutum yana so ya mori kan sa domin idan akace babu ido ga dan Adam komai ya tsaya masa, wannan dalilin yasa muka ga dacewar mu tallafawa al’umma ta wannan bangare”.

Yanzu-yanzu: Hukumar ZaΙ“e ta sauya lokacin yin zaΙ“en kananan hukumomin Kano

Ya ce zai cigaba da ba da irin wannan dama a lokuta daban-daban domin inganta lafiyar al’ummar kananan hukumomin kura Madobi da Garin Malam.

“Daga bisani zamu bada tallafin jari ga al’umma dubada halin matsin rayuwa da al’umma suke ciki a yanzu”.

Talla
Talla

Kazalika Yusuf Datti ya bukaci a’lumma dasu cigaba da Addu’oin samun zaman lafiya tare da fatan samun sauki na matsin rayuwa da Alumma suka tsinci kansu a ciki.

Daga karshe Wasu daga Cikin mutane 3000 da suka amfana da aikin idon kyauta a kura madobi da garin malam sun bayyana farin cikinsu tare da addu’ar Allah yasa aikin ya zama silar warkewar ciwon idon da suke fama dashi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related