Daga Mukhtar Yahya Shehu
Hukumar zabe Mai zaman kanta ta jihar Kano ta sauya lokacin gudanar da zaben kananan hukumomin jihar zuwa watan oktoba.
Kadaura24 ta rawaito Shugaban hukumar faefesa Sani Lawal Malunfashi ne ya sanar da haka yayin Taron masu ruwa da tsaki a Shelkwatar hukumar.
Ya ce sauya lokacin ya biyo bayan bin umarnin kotun koli na tabbatar da ‘yancin gashin Kai ga kananan hukumomin kasar nan daga watan oktoba Mai zuwa.
Faefesa Sani Lawal Malunfashi ya ce hukumar ta Sanya ranar 26 ga watan oktoba na wannan shekara sabanin yadda a baya ta Sanya ranar 30 ga watan Nuwamba Mai zuwa.
Ya ce sauya lokacin gudanar da zaben ya shafi dukkanin lokutan da hukumar ta fitar da suka shafi zaben a baya.

Shugaban hukumar zaben ta jiha ya ce za a fara yakin neman zabe daga ranar 1 gq watan satunba sai Kuma zabukan fitar da gwani daga jam’iyyu daga ranar 3 zuwa 14 ga watan satunba yayin da Kuma za a fara sayar takardun neman tsayawa takara ranar 15 ga watan satunba zuwa 26 ga watan satunba.
Farfesa Sani Lawal Malunfashi ya ce za a gudanar da zaben kananan hukumomin jihar Kano da kansilolin su ranar Asabar 26 ga watan oktoba na wannan shekara yayin da hukumar za ta sanar da sanar da sakamakon zaben ranar 27 ga wata oktoba na wannan shekara.