Inganta Haraji: Gwamnatin Kano ta ba da umarnin rufe duk asusun ma’aikatu

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Gwamnatin jihar Kano ta bada umarnin a rufe dukkanin asusun ma’aikatu da hukumomin gwamnati domin aiwatar da tsarin asusun bai daya.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana haka yayin da yake kaddamar da tsarin tattara kudaden haraji da aiwatar da asusun bai daya a jihar Kano wanda hukumar tattara kudaden haraji ta jiha ta aiwatar.

Talla
Talla

Gwamna Abba Kabir wanda ya nuna damuwarsa kan yadda kudaden harajin jihar Kano suke zurarewa, ya ce gwamnatin jiha ta aiwatar da tsarin ne domin dakile hanyoyin zurarewar kudi wanda zai bawa gwamnati damar gudanar da ayyukan raya kasa da cigaban al’uma.

Ya ja hankalin shugabannin hukumomi da ma’aikatalun jiha dasu yi biyayya ga sabon tsarin, yana Mai jadda cewa gwamnatin jiha zata dauki matakin ladabtarwa ga duk Wanda suka ki yin biyya ga tsarin.

A nasa bangaren, shugaban hukumar tattara kudaden haraji ta jiha Dr. Zaid Abubakar Yace abin takaici ne yadda jihohin Lagos da River suka yi wa jihar Kano zarra duk da kasancewat cibiyar kasuwanci a kasar nan.

Da yake nasa jawabin, shugaban hukumar yaki ta cin hanci da rashawa ta jihar Kano Barr. Muhyi Magaji Rimin Gado yayi alwashin hukumarsa zata yi kafada da kafada da hukumar tattara haraji ta jiha domin dakile zirarewar kudi da kuma hukumar wadanda aka samu da laifin sace kudaden gwamnati.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related