A ranar Alhamis ne labarin hukuncin wata kotun Faransa ya bazu a Najeriya, wadda ta zartar da hukuncin miƙa wasu jiragen Shugaban Najeriya ga wani kamfani na ƙasar Sin.
Tun farko kamfanin ya buƙaci kotun ne ta ba shi damar ƙwace wasu kadarorin gwamnatin Najeriya da darajarsu ta kai ta kuɗi fam miliyan 74.5 da ke ƙasashe takwas na duniya.
Kamfanin Zhongshan Fucheng Industrial Investment Company Limited ne ya nemi buƙatar hakan domin samun diyya kan wata rigimar kwantila da ta shiga tsakaninsa da Gwamnatin Jihar Ogun da ke kudancin ƙasar.
Me gwamnatin Najeriya ta ce?
A nata ɓangare gwamnatin Najeriya ta zargi kamfanin na ƙasar China da yaudarar kotun don cimma wani muradin ko son ranta.
Babban Hadimin Gwamnan Kano ya ajiye Mukaminsa tare da Komawa APC
Cikin wata sanarwa da Bayo Onanuga, mai taimaka wa Shugaban Najeriya kan harkokin yaɗa labarai ya fitar ranar Alhamis, ya yi zargin cewa kamfanin na yunƙurin amfani da yaudara don ƙwace wa ƙasar kadarorinta.
Ya ƙara da cewa kamfanin Zhongshan, “ba shi da gamsassun hujjojin da zai buƙaci Gwamnatin Jihar Ogun ta biya shi kuɗi, saboda a lokacin da aka soke yarjejeniyar, katanga kawai kamfanin ya gina a filin da aka ware masa don gina wurin kasuwancin.”
Bayo Onanuga ya ce kamfanin ya samo umarnin kotu har sau biyu daga Paris a ranar 7 ga watan Maris da kuma ranar 12 ga watan Agusta ba tare da sanar da Gwamnatin Najeriya ko Gwamnatin Jihar jihar Ogun kan shigar da ƙarar ba.
Don haka ina ganin kamfanin ”ya gabatar wa kotun muhimman bayanai wajen yaudarar kotun kan jiragen shugaban Najeriya uku da aka kai Faransa domin yi musu gyara”.
“Matsayin jiragen Shugaban Ƙasa da kuma aikin da suke yi a matsayin kadarorin ƙasa, waɗanda ke da kariyar diflomasiyya, bai kamata kowace kotun waje ta bayar da damar ƙwace su ba,” in ji shi.
Tun yaushe aka shigar da ƙarar?
A shekarar 2016 ce kamfanin na Zhongshan ya shigar da ƙara, bayan da Gwamnatin Jihar Ogun ta soke kwangilar da suka cimma da kamfanin a 2007 na samar da wasu kamfanonin kasuwanci masu sauƙin haraji a jihar.
Sace takardun Shari’a : Ganduje ya yiwa gwamnatin Kano martani
Yunƙurin kamfanin Zhongshan na sake farfaɗo da yarjejeniyar ya gamu da cikas a 2018 lokacin da kamfanin ya garzaya wasu kotunan ƙasar da buƙatar farfaɗo da yarjejeniyar.
To amma a watan Maris ɗin 2021, wata kotu ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ƙotun Ƙolin Birtnaiya, ta yanke hukuncin cewa gwamnatin jihar ta biya kamfanin diyyar Dala miliyan 74.5 , amma sai Gwamnatin Jihar Ogun ta yi biris da hukuncin, ta ƙi biyan diyar.
Jaridar Punch a Najeriya ta ruwaito cewa baya ga jiragen Shugaban Ƙasar uku da aka ƙwace a Faransa, kamfanin na China ya buƙaci kotun ta ba shi damar ƙwace iko da kadarorin Najeriya a ƙasashen Birtaniya da Amurka da Belgium da Canada da Faransa da Singapoe da kuma tsibirin British Virgin Islands.
Haka ma a ranar 14 ga watan Agusta, Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa wata kotun Birtaniya ta bayar da umarnin ƙwace wasu gine-gine mallakin Najeriya a birnin Liverpool da kimarsu ta kai Dala miliyan 1.7 zuwa miliyan 2.2.
Yadda hukuncin ya tayar da ƙura a Najeriya
Wannan batu dai ya janyo ce-ce-ku-ce tare da suka ga gwamnatin Najeriyar tsakanin ‘yan ƙasar musamman ‘yan siyasar hamayya, waɗanda suka ga baiken gwamnatin ƙasar kan hakan.
Daga ciki akwai tsohon ɗan takarar Shugaban Ƙasar na Jam’iyyar LP, Peter Obi wanda ya bayyana ƙwace jiragen Shugaban Ƙasar a matsayin ‘cin fuska’ da gazawa jagororin ƙasar.
Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Mista Obi ya ce wannan batu ya ”tona asirin gwmnatin ƙasar na ci gaba da shirinta na saya wa Shugaba Ƙasar sabbin jirage.
“Duk da irin koke-koke da sukar da aka yi wa shirin gwamnatin Najeriya na saya wa Shugaban Ƙasa jirage a wannan lokaci da ‘yan ƙasa ke cikin halin matsin rayuwa da tattalin arziki, sai kuma yanzu su ɓullo da wannan batu”, in ji mista Obi.
“Ba don yanzu da kotun Faransa ta hana Najeriya ɗaukar jiragen uku ko sayar da su ba, ‘yan ƙasar ba su da wani labari kan sayar da su ko sayo wasu”.
“Biyan kuɗin da ya kai Dala miliyan 100 don saya wa Shugaban Ƙasa jirgi – a ƙasar da ta zama cibiyar talauci ta duniya, wadda ƙananan yaranta da dama ba sa samun damar zuwa makaranta, sannan hauhawar farashin abinci ya kai kashi 40 – babban abun damuwa ne ga al’ummar ƙasar”, kamar yadda Obi ya wallafa a shafinsa na Facebook.
BBC Hausa