Yanzu-yanzu: An sake sassauta dokar hana fita a Kano

Date:

Gwamnatin jihar kano ta amince da sassauta dokar hana fita da aka saka a Kano, inda aka dawo da aka dawo da ta ita daga karfe 6 na yamma zuwa 6 na safe.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, Dogo Salman ne ya sanar da hakan, bayan ganawar hadin gwiwar majalisar tsaro ta jihar karkashin jagorancin Gwamna Abba Yusuf a gidan gwamnati.

Iyayen matashin da yan sanda su ka harba a Ido a Kano na neman Adalci

Kwamishina Salman ya jaddada kudirin gwamnati na wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar tare da sassauta takunkumin hana jama’a damar ci gaba da harkokin yau da kullum.

Ya kara da cewa matakin sassauta dokar ya nuna yadda tsaro ya inganta da kuma kokarin jami’an tsaro na maido da zaman lafiya a Kano.

Gwamna Yusuf ya kuma bukaci al’ummar jihar da su baiwa jami’an tsaro hadin kai tare da bin ka’idojin dokar hana fita domin tabbatar da ci gaba da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dr. Kabiru Getso Ya Mika Ta’aziyya Ga Iyalan Buhari

Daga Rahama Umar Gwaru   Tsohon kwamishinan ma'aikatun lafiya da muhalli...

Gwamnatin tarayya ta ayyana Ranar hutu saboda rasuwar Buhari

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ayyana Talata, 15 ga watan...

Injiniya Iliyasu Usman Salihu ya zama Jakadan zaman Lafiya na Africa

    Injiniya Ilyasu Uasman Salihu, Manajan Darakta na Sadex Engineering...

Halin da ake ciki game da shirye-shiryen jana’izar Buhari

Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda, ya bayayna cewa sai...