Daga Aminu Halilu Tudun Wada
Iyayen wani matashi mai suna Ibrahim Nura Ibrahim wanda ake zargin βyan sanda sun harbe shi a ido yayin zanga-zangar tsadar rayuwa a Jihar Kano suna neman a bi masa haΖΖinsa.
Idan za a iya tunawa kadaura24 ta rawaito ana zargin yan sanda a Kano da harbin matune, wanda hakan ta sa kungiyoyin kare hakkin dan Adam suke ta kiraye-kirayen a gagguta daukar matakin dakatar da harbin, Sannan gwamnatin jihar kano ta kafa kwamitin bincike don gano wadanda suka yi domin hukuntasu.
A jiya litinin dai gwamnan jihar kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya yi alkawarin kafa kwamitin domin gano yadda akai yan sandan suka harbi mutane da dama a Kano, yayin zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa a Kano.
Da dumi-dumi: Ζasar Rasha ta magantu kan Ιaga tutar ta da Ζ΄an Nijeriya ke yi yayin zanga-zanga
Ibrahim Nura wanda yake mazaunin unguwar Tudun Wada ne da ke karamar hukumar Nasarawa ya ce yan sandan sun harbe shi lokacin da yake kan benen gidansu yana korar yara domin su daina bin yan zanga-zanga a jiya litinin.
A zantawarsa da jaridar kadaura24 Ibrahim ya ce bai ji ba bai gani ba , yan sandan suka harbe shi a ido, wanda hakan ya yi Sanadiyar daina ganinsa bayan an yi masa aiki a idon .

” Na ji hayaniyar yan zanga-zangar sun fito daga unguwannin Gama da Tsamiya da Rimin kebe , hakan ta sa na leko ta wundo don hana yara binsu, domin na jiyo wani dan sanda ya na cewa duk wanda ya harba ya harbi banza, kawai Ina tsaye ina yi musu magana sai na ji abu a idona ashe harsashi ne”.
” Ni ban shiga zanga-zanga ba, amma an harbe ni, don haka Ina kira ga gwamnatin jihar kano da sauran kungiyoyin kare hakkin dan Adam da su bi min hakkina Saboda an zalunce ni, ga shi ni maraya ne”. A cewar Ibrahim Nura
Ita ma mahaifiyar matashin ta roki dukkanin masu fada a ji da su taimaka wajen nemawa danta da aka harba ba tare da yayi komai ba hakkinsa.
” Yaron nan ma tun da aka fara Zanga-zangar nan ko wajen baya fita, hasalima da ya ga mun zo zaure ni da kanwarsa haka ya zo yana yi mana fada cewa mu koma gida saboda ka da a biyo yan zanga-zangar ko ayo jifa ko karbi ya sami wani a cikinmu hakan tasa muka koma gida”.
” An ce mu killace ‘ya’yanmu mu hana su shiga zanga-zanga, mun killace su yanzu kuma an zo suna gida ana harbinsu, don haka, Ina kira ga hukumomi da su yiwa Allah su bi mana kadin abun da aka yiwa Ιana.