Yanzu-yanzu: Gwamnan Kano ya kirawo taron majalisar tsaro ta jihar

Date:

Daga Sani Idris Maiwaya

Gwamnan jihar kano Alhaji Abba Kabir Yusuf yanzu haka ya yana jagorantar taron majalisar tsaro ta jihar a gidan gwamnatin jihar kano.

Idan za a iya tunawa kadaura24 ta rawaito cewa an sami hatsaniya bayan da masu zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa suka fito ranar Alhamis domin nuna adawarsa dangane da hanlin da ake cikin na yunwa da fatara a ƙasa baki daya.

Bata gari ne dai suka mamaye titunan jihar kano, Inda suka rika fasa kayan gwamnati da sace kayan al’umma da sauran abubunwan da ba su dace ba.

Wata majiya a gidan gwamnatin jihar kano ta ce fadawa kadaura24 cewa taron majalisar tsaron da ba zai rasa nasaba da halin da ake cikin a jihar ba, Inda aka kwashe kimanin kwana ki 6 ana cikin dokar takaita zirga-zirga, duk da gwamnatin ta sassata dokar Inda ake fita karfe 08 na safe zuwa 02 na rana a kowacce rana.

Waɗanda suka halasci taron majalisar tsaron sun hadar da kwamishinan yan sandan, shugabannin rundunonin soji da shugaban hukumar tsaron farin kaya DSS, sai shugaban hukumar kula da shige da fice da takwaransa na hukumar kula da gidajen gyaran hali.

Sauran su ne mataimakin gwamnan jihar kano da shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jihar kano da dai sauransu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin Sarautar Kano: Fadar Sarki Sanusi ta zargi magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero da kai farmaki Kofar Kudu

Daga Sani Idris Maiwaya   Rikicin Masarautar kano ya na neman...

Shugabannin Kasuwar Kanti Kwari sun shiryawa Gwamnan Kano Addu’o’i na musamman

Daga jafar adam Shugaban kasuwar Kantin Kwari Sharu Abdullahi Namalam...

Dalilin Kwankwaso na kin shiga Hadakar ADC

Jam'iyyar NNPP ta ce abin da ya sa ba...