Daga Ibrahim Sani Gama
Al’ummar jihar Kano suna kokawa da yadda yan Kasuwar jihar Kano musamman Kasuwar Singa suka kara kudaden kayan masarufi a yau bayan bude kasuwar.
Idan za a iya tunawa kadaura24 ta rawaito gwamnatin jihar kano ce ta sanya dokar hana fita bayan da bata gari suka fake da Zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa suka far wa kayan gwamnati da na al’umma a ranar Alhamis 1 ga watan Ugusta.
Tun bayan sassauta dokar hana fitar da gwamnatin jihar kano ta yi, ba a bude Kasuwannin jihar ba sai a yau talata, wanda hakan tasa al’umma suka yi tururuwar zuwa Kasuwar domin yo siyayyar kayan masarufi.
Yanzu-yanzu: An sake sassauta dokar hana fita a Kano
Sai dai a lokacin da al’umma suka shiga kasuwar singa don sayo kayan amfani yau da kullum wadanda suka hadar da Taliya, Makaroni, Fulawa, Magi da sauransu.
Wani mutane mai suna Saminu Ibrahim Kurna ya shaidawa Kadaura24 cewa ya yi mamakin yadda kayan suka yi tashin gwauron zabi ta yadda wasu ma kayan ma ba za sayu ba saboda tsadar da suka yi.
” Kafin faruwar wannan lokaci muna sayan fulawa akan Naira dubu 66 amma yau mun sayeta Naira dubu 77, kuma haka sauran kayiyakin suke duk sun ta shi”. Inji shi
Alhaji Nasiru Farawa wani mai kanti ne a unguwa wanda ya shiga kasuwar domin siyan kayan masarufi a kasuwar ta singa ya ce a bayan yana siyan buhun fulawa akan Naira dubu 65 amma yau an ce masa Naira dubu 85 taliya 15,500 yau kuma Naira dubu 17,80.
” Ni ka ga dole sai hakura na yi da siyan fulawa saboda kudin yayi yawa, gaskiya abun ya yi yawa”.
Malam idris wani magidanci ne da yake zaune a Kano, yace gaskiya akwai bukatar yan Kasuwa su ji tsoron Allah, Saboda abun da suke yi na kara farashin kayan masarufi ba tare da su an kara musu ba, ya sabawa ka’ida .
Da dumi-dumi: Ƙasar Rasha ta magantu kan ɗaga tutar ta da ƴan Nijeriya ke yi yayin zanga-zanga
Muntari Muhammad Liti shi ne mataimakin shugaban kasuwar Singa, da kadaura24 ta tuntube shi don Jin shin ko sun san da abun dake faruwa a kasuwar?, ya ce sun sami labarin yadda wasu yan kasuwar su ke tsauwalawa mutane ta hanyar kara kudin kayansu, inda yace hakan ba daidai bane.
” Abun takaici Mun ji wasu daga cikin yan kasuwar mu suna tsauwalawa mutane a wanna lokaci da ya kamata a saukakawa al’ummar sakamakon mawuyacin halin da suke ciki, gaskiya wannan abun bai kamata ba”.
Ya ce ba duka aka taru aka zama daya ba, akwai wadanda suke ba su tsauwala ba, sana sayar da kayansu yadda aka tafi aka bar shi, “amma mun sami labarin wasu har dubu 85 suke sayar da buhun fulawa, bayan kuma a dubu 64 aka tafi aka bar ta”.
Ya bukaci yan kasuwar da su ji tsoron Allah su rika sassautawa al’umma musamman a wannan lokaci da mutane suka fuskantar ƙarancin kudaden a hannunsu da kuma matsin rayuwa.