Ofishin jakadancin ƙasar Russia a Najeriya ya musanta hannu a cikin amfani da tutar kasar da wasu masu zanga-zanga ke yi.
An hangi masu zanga-zanga na daga tutar ƙasar Russia a yayin zanga zangar a kwanakin nan.

Dama can an zargi ƙasar dai da hannu a rikicin siyasa da ya shafi kasashen Mali da Nijar da Burkina Faso.
Hakan dai ya haifar da damuwa kan shigar wata kasa daga ketare kan al’amuran da suka shafi cikin gida.
Yanzu-yanzu: Tinubu ya dage taron FEC, ya karbi bakuncin shugabannin tsaro
Sai dai a sanarwar da ofishin jakadancin Russia a Najeriya ya fitar ya ce kasar bata shiga al’amuran da suka shafi wata kasa ciki har da Najeriya kuma abinda masu zanga zangar suke yi ya saba da manufofin Russia.
Sanarwar ta kuma ce ƙasar Russia na girmama dimukordiyyar Najeriya.
Daily Nigerian