Daga Sani Idris Maiwaya
Sarkin Kano na 16, Malam Mohammadu Sanusi II, a ranar Juma’a, ya bayyana matukar bakin cikinsa kan ta’addancin da ya faru a Kano a yayin zanga-zangar da aka yi a fadin kasa.
Da yake magana da manema labarai a fadarsa da ke Kano a ranar Juma’a Sanusi ya bayyana rasa rayuka da dukiyoyin da aka yi a matsayin abin takaici .
Sarkin ya jajantawa iyalan wadanda suka rasa ‘yan uwansu tare da yin kira ga iyaye da su sanya ido sosai a kan ‘ya’yansu don gudun kada a yi amfani da su wajen ta da tsarzoma.

Ya kuma bayyana barnar da aka yi a ofishin NCC, inda aka barnata Kaddarori na miliyoyin naira a matsayin koma baya ga jihar Kano.
Sanusi ya jaddada cewa ba masu kishin kano ba ne wadanda suke daukar nauyi ana yin tashe-tashen hankula a jihar .
Atiku ya jinjinawa masu zanga-zanga, ya bukaci Tinubu ya saurari koken jama’a
Ya kuma bukaci al’ummar jihar da su tona asirin masu tada fitina, sannan ya shawarci jama’a da su yi addu’ar samun zaman lafiya, da ci gaba a jihar.
Sarkin ya kuma jajanta wa wadanda suka yi hasarar dukiyoyinsu a yayin zanga-zangar .
Zanga-zanga:APCn Kano ta mayar da zazzafan martani ga kalaman gwamna Abba Kabir
Ya kuma bukaci jama’a da su kai rahoton duk wani ko gungun mutanen da ke yunkurin sayar da irin kayayyakin da suka sato ga ofishin yan sanda mafi kusa domin daukar mataki cikin gaggawa.
Ya kuma jaddada cewa ta yin hakan ne za a fallasa wadanda ke da hannu wajen sata da barna tare da gurfanar da su a gaban kuliya.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa da fari dai an fara zanga-zangar adawa da tsadar rayuwar cikin lumana, daga baya ta rikide zuwa tashin hankali a rana ta farko a Kano.