Sarki Aminu Ado ya fara shirye-shiryen mika bukatun al’ummar Kano ga shugaba Tinubu

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Mai Martaba Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero ya bayyana alhini ga wadanda suka gamu da ibtila’i a lokacin gudanar da zanga zanga a ranar alhamis din data gabata a jihar Kano.

Alhaji Aminu Ado Bayero ya bayyana cewa kamar kowanne lokaci yana bayyana cewa duk lokacin da aka shiga matsi na rayuwa ana son bawa ya zama mai kusantuwa ga Allah ya Kai kukansa domin shi ne zai share masa hawaye.

Talla
Talla

Sarkin yayi Kira ga Al’ummar jihar Kano su zauna lafiya sannan a guji tashin hankali da taba dukiyoyin Gwamnati da na sauran Al’umma.

Zanga-zanga:APCn Kano ta mayar da zazzafan martani ga kalaman gwamna Abba Kabir

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran sarkin Abubakar Balarabe kofar Na’isa ya sanyawa hannu kuma ya aikowa kadaura24.

Tuni dai Mai Martaba Sarkin ya Fara shirye shirye domin jagorantar
tawagar wakilai daga jihar Kano inda zasu tafi domin isarwa da Shugaban kasa koken Al’ummar jihar Kano da suka bashi a lokacin da sukayo tattaki zuwa fadarsa.

A saboda Haka ne Mai Martaba Sarkin Alhaji Aminu Ado Bayero ya sake jaddada bukatar GA Al’umma su cigaba da addu’a, sannan iyaye su kula da tarbiyyar yayansu inda yace Manzon Allah S.A.W yace kowannen ku makiyayi ne kuma za a tambaye shi a kan abin da aka bashi kiwo ranar gobe kiyama.

Daga nan yayi adduar Allah ya jikan wadanda suka rasa rayukansu ya kuma bawa wadanda suka samu raunuka lafiya tareda mayarwa wadanda suka rasa dukiyoyinsu fiye da abunda suka rasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Tinubu ya taya tsohon Gwamnan Kano, Shekarau murnar cika shekaru 70

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon Gwamnan...

Abdulmumin Kofa ya koma APC tare da bayyana goyon bayansa ga Tinubu

Abdulmumin Jibri Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Kiru...

Labari mai dadi: Nahcon ta rage kudin kujerar hajjin 2026

Shugaban hukumar NAHCON Kula da aikin hajji ta Nigeria ...

Shugabannin Hukumomi a Kano Sun Yaba Da Ayyukan Abba, Sun Nemi Ya Nemi Wa’adi Na Biyu

Kungiyar shugabannin hukumomi da ma'aikatun gwamnatin jihar Kano ta...