Daga Sadiya Abba Dala
Kamfanin Dan Iliyasu Satame Global Enterprise da hadin gwiwar wasu yan uwa daga garin Obajana sun shirya taron saukar karatun al’qur’ani mai girma har guda goma da zummar Allah Subhanahu wata’ala ya kara ciyar da kamfanin Ɗangote gaba.
Alhaji Aliko Ɗangote dai shi ne mamallakin rukunonin kamfanin Ɗangote, kuma wanda ya fi kowa arziki a Nahiyar Africa.
Zanga-zanga: Kwamitin zaman lafiya ya yi Allah-wadai da lalata kaddarori a Kano
Kamfanin na Dan Iliyasu Satame Global Enterprise ya ce ya shirya taron saukar al’qur’anin ne da addu’o’in Allah ya kara yalwata arzikin Ɗangote saboda yadda yake tallafawa al’umma ba a Nigeria ka dai ba har da sauran kasashen Africa.
A sanarwar da Babban Nura ya aikowa kadaura24, za a gudanar da taron saukar ne a ranar lahadi 28 ga watan almuharram, 1446. Wcce ta zo daidai da 04 ga watan Ugusta 2024.
Za a gudanar da taron ne a zawiyar Alhaji Umaru Tanko Obajana da misalin karfe 10 na safe.
Sanarwa daga Baban Nura