Daga Rahama Umar Kwaru
Shugaba Bola Tinubu zai yi jawabi ga al’ummar Nigeria a ranar Lahadi, 4 ga watan Agusta, 2024, da karfe 7:00 na safe.
An umurci gidajen Talabijin, Rediyo, da sauran kafafen yada labarai na zamani da su jona jawabin shugaban kasar daga gidan talabijin na kasa (NTA) da Gidan Rediyon Tarayyar Najeriya (FRCN) don yada shirye-shiryen.
Atiku ya jinjinawa masu zanga-zanga, ya bukaci Tinubu ya saurari koken jama’a
Hakan na cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa Ajuri Ngelale ya sanyawa hannu kuma aka rabawa manema labarai.
Sanarwar ta ce za a maimaita jawabin shugaban kasar a NTA da FRCN da karfe 3:00 na rana da 7:00 na yamma a rana guda.