Dalilan ƙazancewar zanga-zanga a arewa

Date:

A ranar 1 ga watan Agusta ne matasan Najeriya suka fara zanga-zangar nuna fushi kan tsadar rayuwa, wadda suka ce za su kwashe kwana 10 suna yi.

Zanga-zangar ta gudana ne a jihohi 26 a ranar Alhamis, inda masu zanga-zangar suka riƙe alluna masu ɗauke da saƙonni daban-daban.

Sai dai wani abu shi ne yadda aka samu tashe-tashen hankula a wasu jihohi, musamman na arewacin Najeriya.

Wannan lamari ya kai ga rasa rayuka da kuma sanya dokar hana fita a kimanin jihohi biyar.

Rahoton kamfanin Beacon, mai nazari kan harkokin tsaro a Najeriya da ƙasashen yankin Sahel ya ce an samu asarar rayukan kimanin mutum 20 a ranar Alhamis kawai.

Tuni jihohin Kano da Borno da Jigawa da Katsina da Yobe suka ayyana dokar hana fita a sassan jihohin.

Talla
Talla

Wannan ya faru ne sanadiyyar arangama da aka samu tsakanin jami’an tsaro da masu zanga-zanga.

Dalilan ƙazancewar zanga-zanga a arewa

Wani abu da ya fito fili shi ne yadda zanga-zangar ta fi ƙazancewa a arewacin Najeriya

Shin me ya haifar da hakan?

BBC ta tuntuɓi Kabiru Adamu, masani kan lamurran tsaro kuma shugaban kamfanin Beacon Consulting.

Talauci

Dalili na farko da Kabiru Adamu ya bayar shi ne talauci.

Duk da cewa akasarin al’ummar Najeriya na rayuwa cikin ƙangin talauci, amma lamarin ya fi ƙamari ne a arewacin ƙasar.

Wani rahoton Hukumar ƙididdiga ta Najeriya na shekarar 2022, ya nuna cewa kimanin kashi 63 cikin ɗari na al’ummar Najeriya na fama da talauci, wato kimanin mutum miliyan 133 ke nan a cikin mutanen ƙasar kimanin miliyan 200.

Rahoton ya ce kashi 65 cikin ɗari – wato mutum miliyan 86 – na masu fama da talauci a Najeriyar na rayuwa ne a arewacin ƙasar, yayin da kashi 35 cikin ɗari ne kawai na matalautan ke rayuwa a kudancin ƙasar.

Raunin shugabanci

Wani abin da ya taimaka wajen rikiɗewar zanga-zangar zuwa tashin hankali a arewacin Najeriya in ji masanin shi ne rashin ƙwaƙƙwaran shugabanci.

A cewar Dakta Kabiru, hatta zaɓaɓɓun ƴan siyasa ƙalilan ne suke da ofisoshi a mazaɓunsu wanda za su riƙa karɓar ƙorafin al’umma.

Hakan a cewar sa ya sanya al’umma na ganin cewa shugabanni ba su damu da su ba saboda haka nan suna da damar yin abin da suka ga dama.

Da dumi-dumi: Gwamnatin jihar Kano ta sassauta dokar hana fita

Taɓarɓarewar tarbiyya

Abu na biyu da Kabiru Adamu ya bayyana cikin abubuwan da suka sanya zanga-zangar ta rikiɗe shi ne taɓarɓarewar tarbiyya.

Ya ce “wannan kuma yana da alaƙa da irin zamantakewar da muke yi…za ka ga cewa a cikin iyalai shi mai gida ba sanya ido yake yi ba kan tarbiyya sosai.”

A cewarsa hakan ya kai ga matasa na ɗaukar shawarwari marasa kyau a tsakanin abokansu ko kuma guraɓatattun mutane.

Shaye-shaye

Wani abin kuma shi ne shaye-shaye, in ji Dakata Kabir Adamu.

Ya bayyana cewa shan ƙwaya “a tsakanin ƙananan yara da kuma mata abin ya yi muni a arewa.”

Bincike ya nuna cewa a arewacin Najeriya ana da yawaitar amfani da miyagun ƙwayoyi, wadanda suka haɗa da maganin tari da kuma wasu ƙwayoyi wadanda ake sha na maganin cutuka.

Haka nan akwai yawaitar masu ta’ammuli da tabar wiwi da sauran kayan maye waɗanda ake haɗawa a gida.

Rashin tsaro

Abu na gaba da Kabiru Adamu ya ambato a matsayin ɗaya daga cikin dalilan da suka sa zanga-zangar ta fi ƙazancewa a arewa shi ne rashin tsaro.

Kusan kowace jiha a arewacin ƙasar na fama da matsalar tsaro, lamarin da Kabiru Adamu ya ce ya sanya mutane da dama sun mallaki makami.

Zanga-zanga: Jihohi 6 da akan sanya musu dokar hana fita a Nigeria

Gwamnatin Najeriya ta nuna damuwa kan tashe-tashen hankula

Gwamnatin Najeriyar ta yi Allah wadai da tashin hankalin da ake samu yayin zanga-zangar ƙuncin rayuwa da aka fara a sassan kasar a jiya Alhamis.

Malam Abdul’aziz Abdul’ziz, daya ne daga cikin masu magana da yawun shugaban Najeriyar ya sahida wa BBC cewa shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu ya san ƴan ƙasar na da ƴancin yin zanga-zangar tare da bayyana ra’ayinsu “amman abin takaici yadda aka fito a sassa daban-daban an ɓige da abubuwa waɗanda ba su bane yakamata agani a akan tituna.”

“An ɓuge da cin zarafin marasa galihu da zubar da jini da kuma yin abubuwa na rashin ɗa’a da kuma rashin daidai, wannan abun gwamnati ta yi Allah-wadai da shi, ganin cewa mutanen da basu ji ba basu gani ba, an ƙuntata masu, anyi wa wasu asarar dukiyoyi, har wasu ma sun rasa rayukansu, har ma da jami’an tsaro.” cewar Malam Abdul’aziz.

Gwamnatin Najeriyar ta ce ba ta san wadanda suka shirya zanga-zangar ba, wadanda ake iya cewa gasu kuma ba a Najeriyar suke zaune ba, shiyasa ba za ta iya tattaunawa da su ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related