Zanga-zanga: Kwamitin zaman lafiya na Kano ya gargaɗi tubabbun yan daba

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Kwamitin zaman lafiya na jihar kano ya ja hankali tare da gargadin tubabbun matasan yan daba game da tada hargitsi ko taba kayan Jama’a yayin zanga-zangar da ake gudanarwa yau Alhamis daya ga watan Augusta 2024, sakamakon tsadar rayuwa, fatara, da yunwa.

Shugaban sakatariyar kwamitin zaman lafiya na jihar Kano Ambasada Ibrahim Wayya, ne ya ja hankalin tare da nusar da matasan a taron da kwamitin yayi da tubabbun han daba da kuma yan jaridu a Kano.

Talla
Talla

Wayya ya jan hankalin tubabbun Matasan yan dabar tare da nusar dasu illar aikata barna ko hargitsi da razana alumma ne, a dakin taro na inganta tsaro da shiyasa dake Nasarawa GRA anan Kano.

Wayya ya ce shugabancin kwamitin ya ce ba zai shiga zanga-zangar da aka shirya gudanarwa a fadin kasar nan ba, sakamakon rashin sanin Jagororin zanga-zangar.

Yadda masu zanga-zanga suka fara kone-kone a kofar gidan gwamnatin Kano

Ya ce kwamitin ya tattauna da tubabbun yan dabar wanda su ka yi masa alkawarin ba za su bada gudunmawa ayi tashin hankali ko barnata dukiyar al’umma ba.

A jawabinsa daya daga cikin jagororin tubabbun yan dabar a Kano mai suna Kamilu Adakawa, ya yi Alkawarin cewa baza su taba tayar da hankalin ko su bada gudunmawa wajen yin wani hargitsi a fadin jihar nan ba.

Da dumi-dumi:Yadda yan sanda su ka tarwatsa matasan da suka yi yunkurin fasha Shaguna a Kano

Ya ce su da mabiyansu za su yi zanga-zangar lumana ne ta hanyar ayyanawa gwamnatin jihar Kano koken su, da kuma halin da wasu da dama a cikinsu suke ciki, na rashin aikinyi, rashin jari, da kuma masu bukatar a maidasu makaranta, wanda Shi ne silar fadawarsu halin da suke ciki.

Adakawa ya kara da cewa sun gamsu da yadda kwamitin zaman lafiyar na Kano ya bada damar kai kokensu ga gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf domin kaiwa ga shugaban kasa.

Taron wanda akayi da Matasan tubabbun yan dabar manya da kanana, ya sami halartar maitaimakawa gwamnan jihar Kano akan harkokin tsaro Aminu Muhammad Getso.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Abubakar Bichi ya bada gudumawar motocin bas 13 ga jami’o’in Kano da taraktoci 11 ga yan mazabarsa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu Dan Majalisar tarayya mai wakiltar karamar...

Rikicin Sarautar Kano: Fadar Sarki Sanusi ta zargi magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero da kai farmaki Kofar Kudu

Daga Sani Idris Maiwaya   Rikicin Masarautar kano ya na neman...

Shugabannin Kasuwar Kanti Kwari sun shiryawa Gwamnan Kano Addu’o’i na musamman

Daga jafar adam Shugaban kasuwar Kantin Kwari Sharu Abdullahi Namalam...