Zagin Kwankwaso: Abdulmumini Kofa ya Gargaɗi Alhassan Ado Duguwa

Date:

Daga Zakaria Adam Jigirya

Ɗan Majalisar Wakilai na mazabar Kiru/Bebeji, Kano, Hon Abdulmumin Jibrin Kofa, ya gargaɗi ɗan majalisa na mazaɓar Doguwa/Tudun Wada, Alhasan Ado Doguwa da kakkausar murya da ya daina zagin jagoran jam’iyyar NNPP na kasa, Senator Rabiu Musa Kwankwaso, PhD, FNSE.

A ’yan kwanakin nan ne dai aka ga Doguwa a wani bidiyo yana sukar lamirin Kwankwaso da magoya bayansa a jihar Kano.

Sai dai da yake mayar da martani yayin wani gangamin magoya baya 5,000 da aka shirya domin raba musu takin zamani da fom ɗin tallafin Naira 150,000 ga gidaje 1,000 da kuma raba sola da takardun aikin yi ga matasan mazaɓarsa da aka yi a gidansa na Kofa ranar Laraba, ɗan majalisar ya gargadi Doguwa da ya mayar da hankali kan aikinsa na majalisa don kuwa akwai su da yawa a gabansa, ya daina furta kalamai marasa tushe kan Kwankwaso, inda ya ce tsohon Gwamnan ba sa’an shi ba ne ta kowacce fuska.

Talla
Talla

A cewarsa, “Ina so in gargaɗi Alhassan Ado Doguwa da ya daina zagin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, saboda muna girmama shi Kwankwaso kuma muna ganin darajarsa a matsayinsa na madubinmu, jagora kuma uba.

“Abin mamaki ne yadda Doguwa, wanda a kwanakin baya aka ji shi yana ta yabon Kwankwaso a bainar jama’a, amma yanzu ya zo yana zaginsa. Hakan ya yi hannun riga da matsayinsa na mutumin da ya daɗe a zauren Majalisar Wakilai. Saboda haka, ina yi masa gargaɗi na ƙarshe da ya bari, idan kuwa bai bari ba, ba za mu yi ƙasa a gwiwa ba wajen ɗaukar matakin da ya dace a kansa.

“Mu ba ya cikin tarbiyyarmu zagin kowa, amma kuma ba za mu zauna mu zuba ido mu ga wani yana zagin ahugabanmu ba,” in ji Kofa.

Ɗan majalisar wanda kuma ya aike da irin wannan gargaɗin ga sauran mutane irin su Doguwa da suke zagin Gwamnan da su ma su bari saboda za su yi duk abin da za su iya yi wajen kare Kwankwaso, Gwamna da gwamnatin Kano, jam’iyyar NNPP da kuma magoya bayan Kwankwasiyya a ciki da wajen jihar Kano.

Ya kuma ƙara da cewa bugun ƙirjin da ɗan majalisar ke yi cewa ya taɓa ɗan majalisa a lokaci ɗaya da Kwankwaso a shekarar 1992 raini ne da cin fuska ga Kwankwason, saboda hanyoyin da suka bi har suka je gidan sun banbanta.

“Kwankwaso ya ya yi aikin gwamnati na tsawon shekara 17 kuma ya yi digirinsa na biyu a Turai, har ma ya fara na uku, kafin ya lashe zaɓe mai cike da hamayya. Kwarewa da gogewarsa ce ta sa aka zaɓe shi a matsayin Mataimakin Kakakin majalisar. Ko ba don komai ba, kasancewar ya yi jagoranci a majalisar sama da shekaru 32 da suka wuce, ya kamata Doguwa ya girmama Kwankwaso,” in ji Hon Kofa.

Rushe Masarautu: Dan Majalisar Tarayya na NNPP Ya Soki Gwamnatin Kano

Ɗan majalisar ya kuma ce Kwankwaso ya taɓa lashe zaɓe, ya halarci taron rubuta kundin tsarin mulki, ya zama Gwamna har sau biyu, ya zama minista, ya zama jakada a yankin Darfur na Sudan, ya zama Sanata sannan ya yi takarar Shugaban ƙasa har sau biyu, yanzu kuma shi ne jagoran NNPP. Ya zama dole Doguwa ya girmama shi.

Ya kuma ƙaryata maganar da Doguwa yake yaɗawa cewa Kwankwaso na ƙoƙarin ingiza jama’a su fita zanga-zanga da cewa ba gaskiya ba ne, saboda tuni Kwankwason ya riga ya bayyana matsayinsa.

Zanga-zanga: Yadda Mu ka gano makarkashiyar ’yan siyasa na haddasa fitina a Kano – Gwamna Yusuf

“A matsayinsa na dattijo a ƙasa, Kwankwaso ya bayar da shawara ga jama’a da su yi amfani da ƙarfin da suke da shi wajen nuna rashin jin daɗi ta hanyar kuri’unsu idan lokacin zaɓe ya zo. Wannan shi ne matsayin Kwankwaso, kuma a bayyane yake,” in ji ɗan majalisar.

Talla

Sai dai Kofa ya ce mutane na da ’yancin yin zanga-zanga, amma idan ya kama za su yi, su yi ta bisa doron doka.

Hon Kofa ya kuma jaddada cewa har gobe Kano ta Kudu ta NNPP ce da Kwankwasiyya.

Daga nan sai ya ƙara jaddada goyon bayansa ga Gwamna da gwamnatin Kano, sannan ya ce sabuwar dokar masarautun jihar ta yi daidai da buƙatun mutanen Kano ta Kudu da ma jihar baki ɗaya.

Ya kuma yi kira ga sauran jama’a, ko magoya bayan NNPP ko na wata jam’iyyar da su riƙa auna maganganunsu da hankali kafin su furta su saboda akwai gwamnati a jihar, ko suna so ko ba sa so.

Ya kuma shaida musu cewa ya dawo da asusun tallafinsa na musamman a mazabarsa wanda a shekarun baya ya rufe shi sakamakon sama-da-faɗin da wasu jagorori suka yi a baya, inda ya sanar da saka Naira miliyan 10 a cikin sabon asusun, waɗanda ya ce za a yi amfani da su wajen gyaran famfuna a mazabar.

Yayin taron dai, ɗan majalisar ya ce tallafin Naira 150,000 na gidaje 1,000 da kuma takin da aka raba daga hannun gwamnatin tarayya suka fito.

Daga nan sai ɗan majalisar ya jinjina wa Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu da Kakakin Majalisar Wakilai, Rt Hon Tajuddeen Abbas saboda ƙirƙiro tallafin kuɗin da na takin zamanin da ya raba wa ’yan mazaɓarsa.

Taron dai shi ne irinsa na biyu cikin ’yan kwanakin nan da ɗan majalisar ya shirya inda ya raba tallafi sannan malamai suka yi addu’o’i na musamman ga Kwankwaso da Gwamna da gwamnatin Kano da Kwankwasiyya da ma Najeriya baki ɗaya.

Daga cikin waɗanda suka halarci taron akwai ɗan Majalisar Jiha na Kiru, Abubakar Tasi’u Rabula, da takwaransa na Bebeji, Ali Mohammed Tiga da kuma shugabanni, mata da matasan yankin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Zargin Almundahana: ICPC zata gurfanar da shugaban hukumar zabe ta Kano da wasu mutum biyu

    Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta (ICPC)...

Dalilin da ya hana ni zuwa Kano tarbar Tinubu – Ganduje

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa,...

Shugaban RATTAWU na Kano ya taya sabbin shugabannin kungiyar na kasa murna

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Shugaban kungiyar ma’aikatan rediyo, Talabijin da...

Dalilina na ziyartar gwamnan Kano Abba – Inuwa Waya

Daga Rahama Umar Kwaru Tsohon Wanda ya nemi Zama Dan...