Kungiyar ‘Ya’yan ‘yan siyasa ta yi Allah wadai da zanga-zangar Kano a gaban Doguwa

Date:

Kungiyar ‘yayan yan siyasar Najeriya reshen jihar Kano ta nisanta kanta daga zanga-zangar da ake yi a fadin kasar sakamakon matsin tattalin arziki da ‘yan Najeriya ke fuskanta.

Shugaban kungiyar Muktar Daula Raula ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan da suka ziyarci tsohon shugaban masu rinjaye na majalisar wakilan Najeriya Alhassan Ado Doguwa a ofishinsa a ranar Talata.

Raula ya ce sun je ofishin Doguwa ne domin su gabatar da kansu a matsayin kungiya da kuma sanar da matakin da suka dauka na yin Allah wadai da zanga-zangar da ake yi, wanda a cewarsu  ba ita ce zata kawo karshen matsalar ba

Daga nan sai shugaban ya bukaci masu zanga-zangar da su rungumi tattaunawa da gwamnati da duk masu ruwa da tsaki domin cimma burin da suka sanya a gaba.

A nasa jawabin, Alhassan Ado Doguwa ya yabawa kungiyar, inda ya bayyana su a matsayin masu hankali kuma shugabannin gobe.

A cewar Doguwa, duk da amincewa da wasu kalubalen da ake fuskanta, amma ya kamata masu zanga-zangar da kuma ‘yan Najeriya su mika kokensu ga ‘yan majalisunsu, na wakilai da kuma sanatoci domin su kuma su mika koken nasu ga gwamnatin tarayya domin daukar matakin gaggawa.

“Duk da halin matsin tattalin arziki da ‘yan Najeriya ke fuskanta, amma bai kamata zanga-zangar ta zama mafita ba, gwamnatin tarayya na bukatar lokaci domin ta bi hanyoyin da suka dace na magance korafe-korafen, na yi imani dukkan ku kuna da ‘yan majalisar jiha daga mazabunku, ‘yan majalisar wakilai.  da Majalisar Dattawa, kowa ya bi ta wajesu kuma na tabbata za a dauki matakan da suka dace,” inji shi.

“Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu, mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima, sakataren gwamnatin tarayya, hatta shuwagabannin mu masu daraja a majalisar dokokin tarayya, shugaban majalisar dattawa da kakakin majalisar wakilai Honorabul Tajudden Abbas sun yarda da cewa ana fama da yunwa da wasu kalubale a ƙasar, amma zuwa titi don yin zanga-zanga bai kamata ba domin ba zai magance matsalolin ba,” in ji Doguwa.

Daga nan sai Alhassan Ado Doguwa ya yabawa shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu bisa amincewa da yayi a kammala aikin titin Kano zuwa Maiduguri a cewar sa sama da shekaru goma sha biyar aka ba da aiki, sai titin Kano Western bypass wanda ya tsaya kusan shekaru takwas da kuma ‘yancin cin gashin kan kananan hukumomin Najeriya wanda shi ne zai zama mabuɗin ci gaban Nigeria.

Doguwa ya yi kira ga al’ummar Nigeria musamman matasa da cewa kada su dauki doka a hannunsu, domin daukar doka a hannu yana lalat kasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rasuwar Buhari: Majalisar Nigeria ta dakatar da duk aiyukanta

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Majalisar dokokin Nigeria ta dage zamanta...

Gwamnati ta baiwa ma’aikata hutu saboda rasuwar Muhammad Buhari

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gwamnatin jihar Katsina karkashin gwamna Umar...

Bayan tura Kashim ya taho da gawar Buhari, Tinubu ya ba da umarnin sassauta Tutar Nigeria

Shugaban kasa Bola Tinubu ya bada umarnin ayi kasa...

Yanzu:yanzu: Tsohon shugaban Nigeria Buhari ya rasu

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un!!! Allah yayi wa tsohon shugaban...