Zanga-zanga: Yadda Mu ka gano makarkashiyar ’yan siyasa na haddasa fitina a Kano – Gwamna Yusuf

Date:

Daga Aliyu Danbala Gwarzo

 

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya koka kan yadda wasu ‘yan siyasa da bai bayyana sunayensu ba ke shirin haifar da tsarzoma a ranar 1 ga watan Agusta a jihar.

Yusuf, wanda ya bayyana hakan a ranar Laraba, ya ce gwamnatinsa ta bankado wani yunkuri da wasu ‘yan siyasa marasa kishi suke yi na fakewa da sunan zanga-zangar domin tayar da tarzoma.

“A shirye muke mu karbi masu zanga-zangar lumana a gidan gwamnati. Ba zan gudu ba, su kawo kokensu zan kaiwa Shugaba Tinubu, mu gabatar masa da matsayinmu,” inji Gwamnan.

Talla
Talla

Ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta sake duba farashin man fetur da wutar lantarki tare da bude iyakokin kasar domin ba da damar shigo da kayayyaki cikin kasar nan.

Yusuf ya kuma bukaci gwamnati da ta rage tsadar kayayyakin masarufi domin saukakawa ‘yan Najeriya.

Karin bayani kan jadawalin zaɓen kananan hukumomi na Kano

“Bari in tuna muku, lokacin da muka hau mulki sai da muka yi iya bakin kokarinmu don tabbatar da dawo da zaman lafiya jihar.

Mun gano wani yunkuri da wasu ‘yan ‘yan siyasa suka yi na sayen jar hula da raba su ga ‘yan daba da za su yi amfani da su a yayin zanga-zangar don yin sace-sace a shaguna mutane wadanda ba su ji ba ba su gani ba,” inji shi.

Gwamnan ya ce gwamnatinsa na shirin samar da ofishin da zai rika kula da farashin kayayyaki a jihar domin tabbatar da an daidaita farashin da kayiyyaki.

Talla

Ya ce gwamnatinsa ta dukufa wajen ganin cewa rayuwa ta zama mai sauki ga talaka, ya kara da cewa gwamnati ta dawo da akwatunan karbar shawarwarin jama’a domin karbar shawarwari kai tsaye daga jama’a.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Halin da ake ciki game da shirye-shiryen jana’izar Buhari

Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda, ya bayayna cewa sai...

Rasuwar Buhari: Majalisar Nigeria ta dakatar da duk aiyukanta

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Majalisar dokokin Nigeria ta dage zamanta...

Gwamnati ta baiwa ma’aikata hutu saboda rasuwar Muhammad Buhari

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gwamnatin jihar Katsina karkashin gwamna Umar...

Bayan tura Kashim ya taho da gawar Buhari, Tinubu ya ba da umarnin sassauta Tutar Nigeria

Shugaban kasa Bola Tinubu ya bada umarnin ayi kasa...