Daga Rukayya Abdullahi Maida
Hukumar zabe mai zaman kan ta ta jihar kano ta bayyana cewa za ta gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi 44 a ranar 30 ga watan Nuwambar 2024.
Idan za a iya tunawa kadaura24 ta rawaito Gwamnan kano Alhaji Abba Kabir Yusuf a kwamakin bayan ya bayyana cewa sun shirya domin gudanar da zaben kananan hukumomin a jihar.

Gwamnan ya bayyana hakan ne Kwanaki kadan da kotun kolin kasar nan ta tabbatar da yancin cin gashin kan kananan hukumomi. Kuma ta ce duk karamar hukumar da bata da zababben shugaba ba zata sami kuɗin ta ba .
Shugaban hukumar Farfesa Sani Lawan Malumfashi ne ya bayyana hakan ga Manema labarai a kano, ranar laraba.
Karin bayani zai biyu baya