Karin bayani kan jadawalin zaɓen kananan hukumomi na Kano

Date:

Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa

 

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Jihar Kano, ta sanar da cewa za ta gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi a ranar 30 ga watan Nuwamba, 2024.

Wannan na zuwa ne bayan hukuncin Kotun Ƙoli da ya bai wa ƙananan hukumomi ‘yancin cin gashin kai tare da buƙatar jihohi su gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi.

A baya-bayan nan, Gwamnatin Jihar, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana aniyar gwamnatin na gudanar da zaɓen nan ba da jimawa ba.

Talla
Talla

A wani taron manema labarai, shugaban hukumar, Farfesa Sani Lawal Malumfashi, ya tabbatar da shirinsu na gudanar da zaɓen.

Ya kuma bayyana cewa za a yi wa dukkanin ‘yan takara gwajin miyagun ƙwayoyi kafin a ba su damar tsayawa takara.

Jadawalin zaɓen zai kasance kamar haka:

_ Fara shirin zaɓen a ranar 15 ga watan Ugusta 2024.

_ Jam’iyyu za su fara tallata hajarzu daga 06 ga watan satumba zuwa 29 ga watan Nuwanba, 2024.

– Zaɓen fidda gwani na jam’iyyu da gabatar da bayanan ‘yan takara: 19  ga watan Satumba zuwa 30 ga watan satumba.

_ Fara sayar da a fom din na gani ina so daga 01 ga watan October zuwa 16 ga watan October, 2024.

_ Tantance yan takara daga 18 ga watan October zuwa 25 ga watan October, 2024.

– Fitar da sunayen ‘yan takara: 15 ga watan Oktoba.

_ Sauya yan takara 25 ga watan October zuwa 1 ga watan Nuwanba, 2024.

Gwamnatin Kano ta musanta labarin kashe Naira Biliyan 10 wajen siyan kayan Ofis

_ Fitar da sunayen karshe na yan takara daga 28 ga watan October, 2024.

_ Zabe ranar 30 ga watan Nuwanba, 2024.

_ Sakamakon zabe daga 30 ga watan Nuwanba zuwa 01 ga watan Disamba, 2024.

_ Idan an sami zaben da bai kammala ba za a yi shi a ranar 14 ga watan Disamba, 2024.

Malumfashi ya ce hukumar su zata hada hannu da hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi NDLEA wajen tantance yan takara.

Ya ce za su dauki wannan matakin ne domin ganin wadanda suke shaye-shaye ba su sami damar tsayawa takarar shugabannin kananan hukumomi ba a kano.

Ya ba da tabbacin za su gudanar da sahihi kuma ingantaccen zabe wanda koya zai yi na’am da shi.

Zaɓen ƙananan hukumomi na ƙarshe a Kano an gudanar da shi ne a ranar 16 ga watan Janairu, 2021 a faɗin ƙananan hukumomi 44 da mazaɓu 484.

Talla

A halin yanzu, waɗannan ƙananan hukumomi na ƙarƙashin jagorancin shugabannin riƙon ƙwarya.

Hukumar zaɓen ta kuma sanar da cewa haramun ne manna fastocin yaƙin neman zaɓe a ginin gwamnati, fada, da wuraren ibada, kuma za ta hana duk wanda ya keta wannan doka tsayawa takara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Labari mai dadi: Nahcon ta rage kudin kujerar hajjin 2026

Shugaban hukumar NAHCON Kula da aikin hajji ta Nigeria ...

Shugabannin Hukumomi a Kano Sun Yaba Da Ayyukan Abba, Sun Nemi Ya Nemi Wa’adi Na Biyu

Kungiyar shugabannin hukumomi da ma'aikatun gwamnatin jihar Kano ta...

Idan mu ka rungumi Addu’o’i ba abun da Amurka za ta iya yiwa Nigeria – SKY

Shahararren ɗan kasuwa a Kano, Alhaji Kabiru Sani Kwangila...

Shugaban APC na Kano Abdullahi Abbas ya Magantu Kan Zargin raba Ramat da Kujerarsa

Shugaban jam’iyyar APC na Jihar Kano, Alhaji Abdullahi Abbas,...