Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Ministan yada labarai da wayar da kan al’umma na kasa, Mohammed Idris, ya ce gwamnatin tarayya ba za ta bayyana wuraren da zata sayar da Shinkafar da ta karyar da farashin ta zuwa Naira dubu 40 ba, saboda gudun ka da masu kudi su je su saye.
Ministan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake amsa tambayoyin manema ranar laraba a Abuja.
Idan za a iya tunawa kadaura24 ta rawaito cewa Gwamnatin Tarayya ta bakin Ministan a ranar Litinin, ta ce ta samar da cibiyoyi a fadin kasar nan inda ‘yan Najeriya za su iya siyan buhunan shinkafa 50kg a kan Naira 40,000.

Idris ya ce wannan shiri na daya daga cikin tsare-tsaren da gwamnatin Tinubu ta fito da su domin saukakawa yan kasa tsadar rayuwa.
Sai dai da yake magana a ranar Larabar da ta gabata, ministan ya ce ana shirin raba buhunhunan shinkafar zuwa jihohin Nigeria.
Karin bayani kan jadawalin zaɓen kananan hukumomi na Kano
Ya kara da cewa, ba za a iya bayyana wuraren da za a sayar da su a fadin kasar nan ba saboda dalilai na tsaro, kuma don tabbatar da cewa talakawa da akai tsarin don su sun sami shinkafar.
“Zai yj wahala a ambaci wuraren da za a sayar da Shinkafar saboda dalilan tsaro.

“Amma muna da shinkafar a kasa, kuma za a sayar da ita a kan N40,000.
“An riga an samu shinkafar, zan iya tabbatar da cewa za a sayar da ita a wurare daban-daban a fadin kasar nan.