Zurarewar Haraji: Majalisar wakilan Nigeria ta yi Sammacin Ɗangote da BUA

Date:

Majalisar Wakilai ta umarci kamfanonin BUA da Dangote su bayyana a gabanta don amsa tambayoyi kan zirarewar kudaden harajin Gwamnatin Tarayya.

Kamfanonin simintin BUA da Dangote na cikin jerin kamfanoni masu zaman kansu da cibiyoyin Gwamnatin Tarayya 113 da za su amsa tambayoyi kan wannan lamari.

Shugaban kwamitin binciken kudaden jama’a na majalisar, Bamidele Salam, ya sanar cewa shugabannin kamfanonin ko manyan akantocinsu ne za su hallara domin amsa tambayoyin.

Rarara ya Magantu AKan Goge Shafinsa da Facebook Ya Yi

Bamidele Salam ya ce binciken zai mayar da hankali ne kan rashin biyan kudaden haraji ga gwamnati, rashin bin ka’idojin da doka ta shimfida wajen biya, da kuma zirarewar kudaden.

Ya ce binciken zai fara ne daga ranar 30 ga watan nan na Yuli zuwa 8 ga Agusta, 2024, kuma majalisar za ta yi tsattsuran hukunci kan duk kamfani ko cibiyar gwamnati da ta ki amsa gayyatar.

Sanarwar ta ce ana bukatar, “kamfanonin su zo da duk takardun da ake bukata.”

Bankunan First Bank, Zenith Bank, Guarantee Trust, Access Bank, Polaris, FCMB, Fidelity da Keystone na cikin masu amsa tambayoyin.

Hakazalika kamfanin hakar mai na Shell Develompent Company da kamfanin lemon kwalba 7Up da kamfanin mai na Durbi Oil.

Talla
Talla

Sauran kamfonin abinci irin su C-Way Food & Beverages da kamfanin madarar Fan Milk da kamfanin Rite Food Ltd; Guinness Nigeria Plc; Pabod Int’l Breweries; Champion Breweries; Agio Power Plant (Kwale Okpai Power Plant); Euro-Global and Disability Plc.

Hukumomi da cibiyoyin gwamnati da za a bincika sun hada da; Ma’aikatar Noma da Samar da Abinci, wadda za a bincika kan zargin karkatar da kudaden tallafin COVID-19.

Da dumi-dumi: Tinubu ya rage farashin Shinkafa a Nigeria

Hakazalika za a binciki Cibiyar Yaki da Yaɗuwar Cututtuka ta Kasa (NCDC) kan zargin karkatar da kudaden yaki da cutar COVID-19.

Hukumar Gidan Radio ta Kasa (FRCN) kuma za ta amsa tambayoyi kan zirarewar kudaden shiga ta kafar Remita.

Sai Majalisar Karamar Hukumar Gwagwalada da za ta amsa tambayoyi kan zargin almundhana da rahoton shekarar 2020 da ofishin babban mai binciken kudi na kasa ya bankado.

Sauran da ake zargi a rahoton sun hada da:

Ma’aikatar Tsaro, Matatar Mai ta Kaduna, Kamfanin Wutar Lantarki ta Kasa na kuma Hukumar Iskar Gas ta Kasa (NLNG) da Ma’aikatar Sufuri ta Kasa

Akwai kuma Hukumar Kula da Kamfanonin Gwamnati (BPE), Ma’aikatar Kasafi da Tsare-tsare, Jami’ar Sojoji da ke Jihar Borno, Ma’aikatar Ma’adinai, Hukumar Kogin Neja Delta, Ma’aikatar harkokin waje, Ma’aikatar Ilimi da Hukumar Jarabawa ta Kasa (NECO)

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Zargin Almundahana: ICPC zata gurfanar da shugaban hukumar zabe ta Kano da wasu mutum biyu

    Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta (ICPC)...

Dalilin da ya hana ni zuwa Kano tarbar Tinubu – Ganduje

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa,...

Shugaban RATTAWU na Kano ya taya sabbin shugabannin kungiyar na kasa murna

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Shugaban kungiyar ma’aikatan rediyo, Talabijin da...

Dalilina na ziyartar gwamnan Kano Abba – Inuwa Waya

Daga Rahama Umar Kwaru Tsohon Wanda ya nemi Zama Dan...