Hukumar Shari’a ta Kano ta ladabtar da wasu magatakardar kotuna da dakatar da wasu ma’aikata

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru

 

A kokarinta na ganin ta tsare kimar bangaren Shari’a, hukumar da ke kula da harkokin shari’a ta jihar Kano ta dauki matakin ladabtarwa a kan wasu magatakardar kotuna guda 6.

A taronta karo na 74 da hukumar ta gudanar a ranar 22 ga watan Yulin 2024, hukumar ta dauki matakin ladabtarwa kan wasu ma’aikatan kotuna shida.

Kakakin Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Kano Baba Jibo Ibrahim ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a.

Talla
Talla

Ya ce kwamitin karbar korafe-korafen al’umma na bangaren shari’a ya binciki karar da aka shigar a kan wasu magatakardar kotuna guda biyu (Mustapha Makama Registran kotun majistiri mai lamba 27 da Yusuf Muhammad Yakasai magatakarda a babbar kotun majistiri mai lamba 14 Gyadi-Gyadi) wadanda suka hada baki tare da karbar kudi N130,000 daga hannun wanda ya shigar da karar, da zummar ba da beli wani wanda ake zargi.

Sanarwar ta ce Kwamitin ya gano abin da suka yi ya sabawa ka’ida da kuma dokar aikinsu.

Zanga-zanga: Abubuwan da Tinubu ya fadawa Malamai da Sarakuna a ganawarsa da su

Ya ci gaba da cewa, hukumar kula da harkokin shari’a bisa shawarar kwamitin ta umurci Mustapha Makama da ya tafi ritayar dole, Saboda an ga bai dace ya cigaba da aikin shari’a ba, yayin da shi kuma Yusuf Muhammad Yakasai wanda aka yi amfani da shi wajen aikata laifin an rage masa mukami.

Zanga-zanga: Bayan ganawa da gwamnoni Tinubu na ganawar sirri da Sarakunan Gargajiya

Hakazalika, Baba Jibo ya kara da cewa, kwamitin ya kuma binciki karar da aka shigar a gabansa kan Salisu Ado (Sakataren Babbar Kotun jihar Kano dake Bompai), Bilya Abdullahi (Babban Magatakarda na Kotu mai lamba 9), Ismail Garba da Auwalu Ibrahim Khalil (dukkaninsu Magatakardar na Kotuna). An same su da laifin hada baki, ba da takardun bogi da ha’inci da Kuma ba da umarni ga wani banki ta hanyar kwaiwayon sa hannun alkalin kotun.

Talla

Hukumar kula da harkokin shari’a bisa amincewa da shawarar kwamitin ta dakatar da ma’aikatan da aka ambata a sama ba tare da bata lokaci ba.

“Hukumar za ta ci gaba da aiwatar da ladabtar da duk wani ma’aikaci da kuskura ya yi abun da zai zubar da kimar bangaren Shari’a, domin kare mutunci da kimar aikin Shari’a .

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Abubakar Bichi ya bada gudumawar motocin bas 13 ga jami’o’in Kano da taraktoci 11 ga yan mazabarsa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu Dan Majalisar tarayya mai wakiltar karamar...

Rikicin Sarautar Kano: Fadar Sarki Sanusi ta zargi magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero da kai farmaki Kofar Kudu

Daga Sani Idris Maiwaya   Rikicin Masarautar kano ya na neman...

Shugabannin Kasuwar Kanti Kwari sun shiryawa Gwamnan Kano Addu’o’i na musamman

Daga jafar adam Shugaban kasuwar Kantin Kwari Sharu Abdullahi Namalam...