Abun da Mahukuntan Nigeria ke yiwa Matatar mai ta Ɗangote ka iya yiwa tattalin arzikin kasar illa – Falakin Shinkafi

Date:

Daga Maryam Muhammad Ibrahim

 

Falakin Shinkafi Amb. Yunusa Yusuf Hamza ya kalubalanci hukumomin man fetur na Nigeria Saboda kokarin zagon kasa da suke yiwa matatar man fetur ta Ɗangote wadda yace hana ta aiki tamkar hana talaka samun sauki ne.

“Waɗannan abubunwan da ake yiwa matatar mai ta Ɗangote babu shakka za su iya kawo cikas wajen shigowar masu zuba hannun jari kasar, saboda duk wanda ya ga ana yiwa dan kasa irin wannan akan wata Sana’a da ya yarda yasa kuɗinsa, to babu shakka Dan wata kasar zai ji tsoron zuwa domin gudun kar a karya shi”.

Falakin Shinkafi ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da ya yi da Jaridar Kadaura24 a ranar talata.

 

Ya ce a kwana baya gwamnatin tarayya har karya darajar naira ta yi saboda masu zuba hannun jari na kasashen waje, amma abun mamaki ga dan kasa ya kashe magudan kudadensa maimakon a taimakasa kuma a gode masa amma an zo ana bin sa da bita da kulli.

Talla

” Wannan matatar man ta Ɗangote babu shakka ita ce matatar mai mafi girma a Africa Kuma Allah ya taimake mu dan kasar mu ne mai ita, kyautuwa ya yi gwamnatin tarayya ta ba shi dukkan wata gudunnawa don ya yi nasara, domin idan ya yi nasara tattalin arzikin Nigeria ma ya yi nasara domin zai kara bunkasa”. A cewar Falakin Shinkafi

Gwamnatin Nigeria ta fara yunkurin sassanta Ɗangote da hukumomin man fetur na kasar

Amb. Yunusa Yusuf Hamza ya bukaci gwamnatin tarayyar Nigeria da ta takawa wadancan hukumomin man fetur na kasar burke, idan kuma da sanin ta ake haka to ta sani yan Nigeria ba za su lamunci kawo cikas akan abun da zai kawo musu sauki ba.

” Bawan Allah nan ya zo ya yi wannan matatar domin tace man fetur da Gas da sauransu don yan Nigeria su sami sauki amma an zo sai tuhume-tuhumen ake masa, ko karya shi ake so ayi ko so ake ya rufe mu ba mu gane ba, kuma gwamnati Kullum tana cewa yan kasuwar duniya su zo su saka hannun jari a ƙasar ta ya hakan zai yiwu”. Inji Falakin Shinkafi

Talla

Falakin Shinkafin wanda shi ne jarman matasan Arewacin Nigeria ya bukataci gwamnatin tarayya da ta dauki matakan da suka dace domin shawo kan matsalar don cigaban yan kasa da tattalin arzikin Nigeria.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamna Abba Ya Sanya Hannu Kan Dokar Kafa Gaya Polytechnic

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sanya...

Sojoji sun mikawa Tinubu Shawarwari yadda za a kawo karshen matsalar tsaron Nigeria

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya karɓi rahoton dakarun sojan...

Shugaba Tinubu ya sake nada Buba Marwa a matsayin shugaban NDLEA

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sake tabbatar da nadin...

Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa Ya Koma Jam’iyyar APC a Hukumance

Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar...