Daga Aliyu Danbala Gwarzo
Babbar kotun tarayya da ke Kano ta yi watsi da duk wani mataki da gwamnatin jihar Kano ta dauka na soke dokar masarautar Kano.
Idan za a iya tunawa kadaura24 ta rawaito Majalisar dokokin Kano ta soke dokar bayan haka Gwamna Abba Kabir Yusuf ya aiwatar da ita ta hanyar tsige Alhaji Aminu Ado Bayero a matsayin Sarkin Kano.
Gwamnan ya kuma rushe masarautu hudun da suka hada da Bichi da Rano Karaye da kuma Gaya, wanda tsohon gwamnan jihar kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya samar.
Gwamnan ya dogara da dokar ne wajen sake nada Sarkin Kano na 14, Muhammadu Sanusi II, wanda Ganduje ya tsige a shekarar 2020, a matsayin Sarkin Kano na 16.
Rikicin Sarautar Kano: Yan Sanda sun Gargaɗi Mafarauta yan Banga da sauran jama’a
Sai dai Aminu Babba Danagundi, Sarkin Dawaki Babba, ya kalubalanci tanade-tanaden dokar, ya kuma bukaci kotun ta bakin lauyansa, Chikaosolu Ojukwu (SAN), ta yi watsi da sabuwar dokar.
A hukuncin da ya yanke a ranar Alhamis, mai shari’a Abdullahi Muhammad Liman, ya yi watsi da matakin da gwamnatin Kano ta dauka, inda ya umurci dukkanin bangarorin da abun ya shafa da su ci gaba da kasancewa a matsayin su .
Garin bayani na nan tafe…
Daily trust