Shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano, Alhaji Abdullahi Abbas ya ce babu wata barazana daga jagoran jam’iyyar NNPP Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da za ya iya tsoratar da gwamnatin tarayyar Najeriya.
Abbas ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar yayin da yake mayar da martani ga zargin da Kwankwaso ya yi wa gwamnatin tarayya da jam’iyyar APC na yunkurin kyankyasar sabbin yan boko Haram a Arewacin Najeriya.
Kwankwaso ya bayyana haka ne a wajen bikin kaddamar da aikin gina titin karkara mai tsawon kilomita 85 a mahaifarsa Madobi kan kudi naira biliyan 21.
Ya ce: “jagoran jam’iyyar NNPP wanda yake cikin damuwa sakamakon yadda gwamnatin jihar kano ta kasa tabuka komai, ya kamata jami’an tsaro su kama shi domin ya shaida musu wadanda ke daukar ‘yan ta’addan Boko Haram.
“Muna so mu yi kira ga jami’an tsaro da kakkausar murya da su kamo wannan mutumi domin ya bayyana sunayen wadanda ya kira makiyan jihar da ke aiki da gwamnatin tarayya wajen daukar ‘yan ta’addan Boko Haram da masu tayar da kayar baya.” Inji Abdullahi Abbas
Fadar Shugaban kasa ta mayar wa Kwankwaso martani kan rikicin masarautar Kano
Abdullahi Abbas ya kara da cewa wadannan kalamai na Kwankwaso da ‘yan kungiyarsa zasu iya kawo tashin hankali a Kano.
“Kwankwaso ya dade yana barazana ga Kano da kasa baki daya idan akai la’akari da abubuwan da suka faru a baya. inda ake zarginsa da daukar matasan da galibin su wadanda suka daina zuwa makarantu ne domin tada zaune tsaye a jihar.”
Abbas ya kara da cewa, kafin zaben 2023 da kuma lokacin zaben, an dauki dubban irin wadannan matasa aiki tare da ba su damar tsoratar da jama’a da ba su ji ba ba su gani ba, ta hanyar kai hare-hare, da lalata dukiyoyin da ake ganin na ‘yan adawa ne da kuma kwace wayoyin jama’a.
Shugaban ya ci gaba da cewa, a lokacin da aka dade ana tafka shari’a kan zaben gwamna, Kwankwaso da mukarrabansa sun yi barazanar kashe alkalan kotun sauraren kararrakin zabe idan sakamakon bai yi musu dadi ba.
Abbas ya ce tun bayan hawan Sarki Sanusi Lamido Sanusi, an dauki daruruwan yan daba masu dauke da makamai tare da jibge su a fadar Sarki, inda ake sayar da duk wasu haramtattun kayayyakin maye a fili, lamarin da ke zama barazana ga mazauna cikin fadar da kewaye.
Daily News24