Sallah: Minista Gwarzo ya roki alhazan Nigeria da su yiwa Nigeria da Tinubu addu’a

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Karamin Ministan Gidaje da Raya Birane, Abdullahi Tijjani Gwarzo, ya yi kira ga alhazan Najeriya da ke Saudiyya da su yi wa kasar nan addu’a da kuma samun nasara ga gwamnatin shugaba Bola Ahmad Tinubu.

Ministan ya yi wannan roko ne a sakonsa na Barka da babbar sallah ga ‘yan Najeriya. Ya taya daukacin al’ummar Musulmi murnar zagayowar bikin babbar sallah ta bana tare da nuna kwarin gwiwa cewa Shugaba Bola Ahmad Tinubu zai yi iya kokarinsa wajen ganin ya cika alkawuran da ya daukar wa ‘yan Najeriya.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban mataimaki na musamman ga karamin ministan Adamu Abdullahi ya sanyawa hannu kuma ya aikowa kadaura24.

Gwamnatin Kano ta koka da yadda yan sanda ba sa bin umarnin gwamna

Gwarzo ya bayyana cewa shugaban kasa Bola Tinubu yana kan turbar da ta dace na fitar da kasar nan daga cikin matsalolin tattalin arziki da suka gada daga gwamnatocin da suka gabata, ya kara da cewa an bullo da tsare-tsare masu kyau da dama don inganta rayuwar ‘yan kasa.

Ya bayyana cewa gwamnatin ta bullo da shirye-shirye wadanda ke da tasiri kai tsaye ga al’umma kamar su Shirin Asusun Gidajen Jama’a, Shirin Wayar da Abinci na Uwargidan Shugaban Kasa da dai sauran su da nufin inganta rayuwar ‘yan kasa.

Ba zan damu ba idan wani gwamnan ya zo ya cire ni — Sarki Muhammadu Sanusi ll

Minista Gwarzo wanda ya bayyana damuwarsa kan halin da ake ciki na kalubalen tsaro da al’ummar kasar ke fuskanta, ya kuma tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa, shugaba Tinubu zai ci gaba da yin iya kokarinsa wajen ganin an tabbatar da tsaro a kasar nan.

Ya kuma bukaci ‘yan Najeriya da su kara yi wa kasar addu’o’in samun zaman lafiya da karuwar tattalin arziki da kuma sadaukarwa domin shawo kan kalubalen da ke dakile ci gaban al’umma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dalibai 22 sun kammala karatu da daraja ta 1 a bikin yaye ɗalibai na farko na Jami’ar Baba-Ahmed Kano

Jami’ar Baba-Ahmed, Kano ta gudanar da bikin yaye ɗalibai...

Rundunar Sojin Amuruka ta kammala tsara yadda za ta kawo wa Nigeria hari

  Rundunar sojin Amurka da ke Afirka, AFRICOM, ta gabatar...

Kalaman Trump: Gwamnatin Nigeria ta Fara tattaunawa da Gwamnatin Amuruka

Gwamnatin Najeriya ta ce a gwamnantance tana tattaunawa da...

Ba zan bar Siyasa ba har lokacin da zan bar Duniya – Mal Shekarau

Tsohon Gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau ya ce...