Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa
kungiyar ‘yan jarida ta kasa reshen jihar ta Kano ta ce ta na taya al’ummar musulmi murnar zagayowar bukukuwan Babbar Sallah.
Kungiyar tana kira ga al’umma da su yi koyi da koyarwar Annabi Muhammad (SAW) da ta hada da, hakuri son juna da zaman lafiya .
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar Abbas Ibrahim da sakatariyen kungiyar Abba Murtala suka sanyawa hannu kuma aka aikowa kadaura24.
Hotunan Yadda Sarki Aminu Ado Bayero ya halarci sallar idi a gidan sarki na Nassarawa a jihar Kano
Kungiyar ta NUJ ta jaddada bukatar ‘yan kasuwa su yi taka-tsan-tsan wajen kara farashin kayayyakin masarufi, yayin da ya kamata ‘yan siyasa su gyara dabi’unsu don ci gaban al’umma.
Kungiyar ta kuma taya Gwamna Abba Kabir Yusuf da Malamai da Sarakunan gargajiya da sauran su murnar Barka da Sallah.
Sallah: Minista Gwarzo ya roki alhazan Nigeria da su yiwa Nigeria da Tinubu addu’a
Kungiyar ta NUJ yayin da take jajanta wa jama’a kan mawuyacin halin da tattalin arzikin kasar yake ciki, ta yi kira ga hukumomi da su gaggauta samar da ingantacciyar hanyar da za ta magance wannan lamari.
Majalisar ta jaddada bukatar kowa ya kasance mai bin doka da oda, iyaye su rika lura da unguwanninsu musamman a lokutan bukukuwan Sallah.Ta yi addu’ar Allah ya ba da ikon gudanar da bukukuwan sallar babba da kuma damina mai albarka.