Daga Samira Ahmad
Kungiyar wakilan kafafen yada labaran Nigeria dake aikin a Kano ta ce ta janye takunkumin da ta kakabawa gwamnatin jihar Kano saboda masalayar al’ummar jihar.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar Alhaji Aminu Ahmed Garko ya sanyawa hannu kuma aka aikowa kadaura24.
Sanarwar ta ce kungiyar ta dauki matakin janye takunkumin ne jim kadan bayan wani taron gaggawar da ta gudanar domin duba batun kauracewa aiyukan gwamnatin Kano har na tsahon kwanaki 14 .
Hotunan Yadda Sarki Sanusi II ya gudanar da Sallar idi a masallacin Juma’a na Kofar Mata dake Kano
Idan za a iya tunawa kadaura24 ta rawaito kungiyar ta ce ta dauki wancan matakin ne domin nuna rashin amincewa da yadda gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf ke tafiyar da harkokin gwamnati da kuma yadda take mu’amalantar Manema labarai a jihar.
“Mun fahimci ce ce matakin da muka dauka na kauracewa aiyukan gwamnatin Kano Zai shafi al’ummar jihar musamman a irin wannan lokaci da Ake samun rikicin Sarauta , don haka muna janye takunkumin”. A cewar Garko
Hotunan Yadda Sarki Aminu Ado Bayero ya halarci sallar idi a gidan sarki na Nassarawa a jihar Kano
Kungiyar ta ce yanzu saboda al’ummar jihar Kano zasu cigaba da daukar rahotonnin gwamnatin, amma sun ce za su tabbatar da cewa gwamnatin tana sauke nauyin da al’ummar suka dora mata.
“Mun yaba da fahimta da goyon bayan da jama’a suka ba mu a wannan lokaci, kuma mun yi alkawarin sake sadaukar da kan mu ga aikin da kundin tsarin mulki ya ba mu na fadakarwa da wayar da kan jama’a.”