Kungiyar malaman jinya da ungozoma ta kasa reshen jihar Kano ta Koka da yadda gwamnatin jihar har yanzu taki yi musu ko tayi game da sabbin alawus-alawus da ake baiwa yan kungiyarsu a duk fadin Nigeria.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwar bayan taro da mai rikon mukamin Sakataren kungiyar na jihar kano Kwamaret Ahmad Hamzat Sharada ya sanyawa hannu kuma aka aikowa kadaura24.
Sanarwar ta ce shugaban kungiyar Muhammad Ibrahim mai karfi ya ce akwai wasu alawus-alawus da tuni biyansu ya zama doka , amma har yanzu gwamnatin jihar kano bata ce musu komai akai ba.
Kotun Ta Baiwa EFCC Umarni Akan Kwankwaso
” Mun lura da cewa rashin biyan mambobin mu wadanan alawus-alawus shi ne yake rage musu karsashi wajen gudanar da aikin su, don haka muke kira da gwamnatin da ta dauki matakan da suka dace don ganin an fara biyanmu wadancan kudade, duk da dai muna yabawa gwamnatin saboda yadda take biyan albashi akan kari kuma ba tare da an yankewa kowa komai ba”.
Sanarwar ta ce Abu na biyu cikin abubunwan guda uku da suka cimma shi ne ƙarancin malaman jinya da ungozoma da ake fama da shi a jihar kano, kungiyar ta ce akwai bukatar gwamnatin ta kara daukar wasu aikin don cike gurbin wadanda suka bar aiki da kuma wadanda suka bar kasar suka koma wasu Kasashen don gudanar da aiki.
Yan Jaridu Sun Kaurace wa Harkokin Gwamnatin Jihar Kano
“Babu shakka mun san irin kokarin da gwamnatin jihar kano ta ke yi wajen kula da ilimin kiwon lafiya, to Amma ya kamata a kara sanar da ma’aikata domin yin hakan zai rage yawan samun mace-macen Mata masu juna biyu da sauran su”. A cewar Sanarwar
Ya ce kara inganta aikin su da walwalar ma’aikatan zata kara taimakawa wajen inganta rayuwar al’ummar jihar kano baki daya.
Sanarwar ta ce daga cikin abubunwan da suka cimma a yayin zaman nasu , sun gano akwai matsalar ruwa a jihar kano, wadda tana kara taimakawa yaduwar cututtuka, don haka suka yi kira ga al’umma da su rika taimakawa kokarin gwamnatin jihar kano kasancewar Abubuwa sun yi mata yawa.
” Mu ne muke da kwarewa waje kula da marasa lafiya, don haka Mun gano rashin ruwa ya taka rawar gani wajen kara samun marasa lafiya a jihar, kuma idan aka dauki matakan magance matsalar ruwa to ko shakka babu za a sami saukin masu kamuwa da cututtuka”.
Kungiyar ta bukaci ya’yanta da su kara hakuri su cigaba da jajarcewa wajen aikin su, shugabannin kungiyar suna zama da gwamnatin jihar Kano don warware matsalolin da suke fuskanta cikin lumana.