Ranar Litinin din nan ce ranar da hukumomin ƙasar Saudiyya suka tsayar mastayin ranar cikar wa’adin kammala jigilar maniyyata aikin Hajjin bana daga kowace kusurwa ta duniya.
Da karfe 12 na tsakar daren yau Litinin agogon Saudiyya ne hukumomin na Saudiyya suka ce za su rufe filayen jiragen saman ƙasar 6 ga saukar duk wani jirgin da ya dauko maniyyata daga kowace kasa ta duniya.
Hakan ya sa ƙasashe musamman waɗan da ke da adadi mafi yawa na maniyyatan da ke rige-rigen ganin sun kammala jigilar maniyyatansu kafin cikar wa’adin.
Filayen jiragen su ne waɗan da aka keɓe domin jigilar maniyyatan na bana da ke biranen Riyadh, da Jiddah, da Madina, da Dammam, da Taif, da kuma Yanbu’u.
Kwankwaso ya bayyana wadanda suka hana gwamnan Kano sakat tsawon Shekara Daya
Sai dai hukumomin sun ce rufewar ba za ta shafi jiragen da suka ɗauko fasinjojin da za su shiga ƙasar domin kasuwanci, da yawon bude ido, da ziyaratar ƴan uwa da dukkan wata lalura da ba ta shafi aikin Hajji ba.
Yanzu haka dai ƙasashe duniya na ta fadin tashin ganin sun kammala jigilar maniyyatansu kafin cikar wannan wa’adin da hukumomin saudiyyan suka ɗibar musu.
Muhuyi Magaji ya fara bincike kan badakalar kudaden tallafin da gwamnan Kano ya baiwa matasa
Ranar Litinin din nan ce ranar da hukumomin ƙasar Saudiyya suka tsayar mastayin ranar cikar waadin kammala jigilar maniyyata aikin Hajjin bana daga kowace kusurwa ta duniya.