Daga Aliyu Danbala Gwarzo
Shahararren Malamin Addinin Musulunci nan Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya bukaci a bar shari’a ta yi aikin ta game da batun rikicin masarautar Kano.
“Muna sanar da al’umma cewa shi shehi a konne lokaci yana goyon bayan gaskiya ne, don haka akan wannan lamari na masarautar Kano ya ce a bari gaskiya ta yi halinta tunda al’amarin yana gaban kotu”.
Sheikh Ibrahim Dahiru Bauchi ne ya bayyana hakan yayin wata ziyarar mabaya’a da suka kaiwa Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero da gidan sa dake Narasawa a birnin kano.

Sheikh Ibrahim Dahiru Bauchi ya ce sun je fadar sarkin Aminu Ado Bayero ne don su yi masa fatan alkhairi kuma su yi masa addu’o’in samun nasara kan wannan dambarwar da take faruwa ta masarautar Kano.
Yace yan uwansa da suka je fadar sarkin kano na 16 Malam Muhammadu Sanusi na II a jiya litinin sun je ne ba da yawun shehu Dahiru Bauchi ba.

” Shi Aminu dama aboki ne ga Khalifa Muhammad Sanusi II, kuma ya fada mana cewa zai zo kano domin ya gana da gwamnan jihar Kano ta karkashin wata kungiyar su, amna bai ce mana zai je gidan sarki ba”.
Sheikh Ibrahim Dahiru Bauchi ya baiwa sarki Aminu Ado Bayero kyautar alkyabba da charbi daga bisani kuma aka karanta al’qur’ani da addu’o’i ga Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero.

Malamin da tawagar sa bisa rakiyar Sarkin Aminu Ado Bayero sun ziyarci hubbaren Sarakunan kano dake gidan Nasarawa inda aka yi musu addu’o’in samun Rahamar Allah subhanahu wata’ala.