Daga Rukayya Abdullahi Maida
Kungiyar kwadago ta kasa ta kashe babban layin wutar lantarki na Nigeria a ranar farko da ta fara yajin aikin sai baba-ta-gani domin nuna adawa da gazawar gwamnati wajen biyan mafi karancin albashi ga ma’aikata.
Bayan tataunawar da kungiyoyin kwadago suka yi sun bukaci a basu N494,000 a matsayin mafi karancin albashi amma gwamnatin tarayya ta ce za ta iya biyan N60,000 ne kawai.
Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa Mohammed Idris, ya ce N494,000 mafi karancin albashi na kasa da kungiyoyin kwadago ke nema, wanda adadin ya kai Naira tiriliyan 9.5 zai gurgunta tattalin arzikin kasar tare da kawo cikas ga rayuwar ‘yan Najeriya sama da miliyan 200.
Yadda Yajin Aikin Yan Kwadago Yasa Maniyyatan Najeriya Cikin Rashin Tabbas
A cikin wata sanarwa da ta fitar da sanyin safiyar Litinin din nan, Kamfanin Dakon wutar lantarki na Najeriya (TCN) ya sanar da ‘yan Najeriya cewa an kungiyar Kwadagon ta kashe babban layin wutar lantarki na Nigeria.
“Kamfanin dakon wutar lantarki na Najeriya yana sanar da jama’a cewa kungiyar kwadago ta kashe babban layin wutar lantarki na kasa, lamarin da ya haifar da kasar ta kasance cikin duhu sa tun da misalin karfe 2:19 na safiyar yau, 3 ga Yuni, 2024.”
Sanarwar tace yan kungiyar Kwadagon sun kori dukkan ma’aikatan dake kula da babban layin na Benin har ma da raunata wasu daga cikin ma’aikatan .
Bikin cika Shekara 1: Gwamna Yusuf zai ayyana dokar ta baci kan ilimi a Kano
“Sauran tashoshin TCN da kungiyar kwadago ta rufe sun hada da Ganmo, Benin, Ayede, Olorunsogo, Akangba da karamar tashar Osogbo”.
Kungiyar Kwadagon dai ta yi hakan ne a Kokarin na tabbatar da dukkanin muhimman wurare a kasar sun kasance a rufe domin yajin aikin yayi armashi da kuma nunawa gwamnatin tarayya adayarsu da gazawarta wajen biyan mafi ƙarancin albashi.