Daga Sani Idris Maiwaya
Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, na shirin kafa dokar ta-baci a fannin ilimi, da nufin kara kaimi wajen inganta harkokin ilimi da tabbatar da ingantaccen ilimi ga kowa da kowa a Kano.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya aikowa kadaura24 a ranar Lahadi.
Rikicin Sarauta: Mazauna Birni Kano sun koka bisa matsalar tsaro
Gwamnan wanda ke shirin kafa dokar ta-baci a ranar Talata, ya ce yin hakan ya na daya daga cikin muhimman alkawuran da yayi lokacin yakin neman zabensa Wanda ya sanya cikin kundin manufofin sa mai suna “Alkawarina ga Kano,” wadda aka tsara kuma aka gabatar wa jama’a 2022, gabanin zaben 2023.
“Sanarwar dokar ta-baci a fannin ilimi na da nufin gaggauta daukar matakai na samar da ayyuka domin tabbatar da samun ingantaccen ilimi ga kowa da kowa a Kano.”
Hisbah ta bayyana dalilin kama jarumim TikTok G-Fresh Al-ameen
“ Gwamna Abba Kabir Yusuf ya shirya tsaf domin kafa dokar ta-baci a fannin ilimi domin a gaggauta yin garambawul a fannin tare da ba da shawarar yadda za a magance kalubalen da ake fuskanta a yanzu a manyan makarantu, Sakandare, da Sakandare da firamare a jihar.” Sanarwar ta ce.
Taron mai zuwa zai tara duk masu ruwa da tsaki a harkar ilimi da suka hada da ministan ilimi, gwamnonin wasu jihohi, da wakilai daga bangaren ilimi da kafofin watsa labarai.
An shirya gudanar da taron ne a ranar Talata 4 ga watan Yuni, 2024, a filin taro na gidan gwamnati dake Kano, za a watsa shi a gidan Talabijin na Channels TV da gidajen Talabijin na cikin gida daban-daban.