Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Jami’an hukumar Hisbah a Kano sun kama shahararren jarumin TikTok, Garba, wanda aka fi sani da G-Fresh Al-amin.
Daily News 24 ta ruwaito cewa, Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama tare da tsare G-fresh bisa zargin yin kalaman da bai dace ba.
Rikicin Sarauta: Mazauna Birni Kano sun koka bisa matsalar tsaro
Da yake tabbatar da kama shi ga jaridar Daily News 24, OC Malam Ali Usman ya bayyana cewa an kama G-fresh din ne saboda karatan Fatiha dake cikin Al-kur’ani mai tsarki ta hanyar da ba ta dace ba yayin bikin Karamar Sallah.