Daga Isah Ahmad Getso
Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta ce ta kama wasu Matasa maza da mata guda 20 bisa laifin yin wanka tare.
Jami’an rundunar ‘Operation Kau Da Badala’ sun kama su ne a wani wurin shakatawa da ke kan titin ring road sakamakon korafin da mazauna yankin suka yi.
Hasashen yanayin da zai kasance yau talata a birnin Kano da wasu jihohin Nigeria
Mataimakin babban kwamandan hukumar, Dakta Mujahidin Aminuddin Abubakar, ya ce laifin ya saba wa dokar Hisbah domin ta hana hada maza da mata a cikin ruwa domin yin wanka.
Hajj 2024: Gwamna Yusuf ya kara goron Sallah ga mahajjatan Kano
Ya nuna damuwarsa kan lamarin, Inda ya ce kamata yayi wanda a cewarsa, za a iya maye gurbinsa da wani aiki mai fa’ida da zai samu lada a wajen Ubangiji.
Ya ce idan an kammala bincike za a hukunta wadanda ake zargin, sannan ya yi kira ga iyaye da su rika sanya ido sosai kan harkakin ‘ya’yansu.