Daga Aliyu Danbala Gwarzo
Hukumar zaɓen ƙasar Chadi ta sanar da Mahamat Idriss Deby a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban kasar wanda aka kada kuri’u a ranar litinin.
Muhammad Idriss Deby dai da ne ga tsohon shugaban kasar Idriss Deby wanda yan ta’adda suka kashe a shekarun baya, kuma shi ya jagoranci ƙasa bayan mutuwar Mahaifin sa a karkashin mulkin Soji.
An ayyana Deby a matsayin wanda ya lashe zaɓen bayan ya samu kaso 61% cikin 100 na kuri’ar da aka kada a zaben.
Hasashen yanayin da zai kasance yau Juma’a a birnin Kano da wasu jihohin Nigeria
Abokin karawarsa wanda kuma shi ne Firaministan ƙasar wato Succes Masra ya sami Kaso 18.53 cikin 100 na kuri’u da aka kasa.
Harajin Tsaron Intanet: Cikakken Bayanin Umarnin da Majalisa ta Baiwa CBN
Tuni dai sabon zababben shugaban kasar Muhd Idriss Deby ya yiwa yan kasar jawabi a kafofin yada labaran Kasar.