Kungiyar ASUU ta yiwa gwamnatin Kano barazanar shiga yajin aiki a Jami’ar Maitama Sule

Date:

Kungiyar Malaman Jami’o’i, ASUU, reshen Jami’ar Yusuf Maitama, reshen Kano, ta koka kan rikicin da ke shirin kunno kai, idan har gwamnatin jihar kano ta gaza magance bukatunta.

Kungiyar ta yi zargin cewa gwamnatin jihar ta shafe watanni tana yin watsi da bukatunsu.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwar hadin gwiwa da shugaban reshen da kuma sakataren kungiyar Mansur Sa’ id da Yusuf Gwarzo suka sanya wa hannu a yau Alhamis a Kano.

Hajjin bana: Yadda Hukumomin Saudiyya suka tarbi rukunin farko na maniyatan bana

Ya ce bukatunsu guda uku ne wadanda suka hada da inganta yanayin aiki ga mambobinsu.

Hasashen yanayin da zai kasance yau Alhamis a birnin Kano da wasu jihohin Nigeria

Sauran kuma sun haɗar da bunƙasawa da kuma hanzarta samar da ci gaban jami’ar ta hanyar bayar da kuɗaɗen aiki mai ɗorewa, ƙarfafawa da kare ikon cin gashin kai na jami’a da ƴancin ilimi.

Kungiyar ta ce ba ta so ta baiyana yanayin a fili ba amma kokarin da gwamnatin jihar ke yi na ganin ta biya musu bukatunsu ya ci tura.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...