Hajjin bana: Yadda Hukumomin Saudiyya suka tarbi rukunin farko na maniyatan bana

Date:

Daga Isa Ahmad Getso

 

Rukunin farko na maniyata aikin hajjin bana sun Isa ƙasa mai tsarki a wannan rana ta alhamis domin gudanar da Ibadar aikin hajjin Shekara ta 2024.

Kadaura24 ta rawaito rukunin farko sun je kasar Saudiyya ne daga kasar India Inda suka sauka a garin Madina domin fara gudanar da ziyara gabanin su wuce garin makka inda acan ne ake gudanar da aikin hajjin.

Maniyatan ƙasar ta India sun sami kyakykyawar tarba daga jami’an hukumar Kula da aikin hajji da umrah ta Kasar Saudiyya.

Hasashen yanayin da zai kasance yau Alhamis a birnin Kano da wasu jihohin Nigeria

An tarbe shi a filin jirgin Sama na Madina Inda aka rika sanya musu Fulawa tare da basu dabino da sauran kyaututuka duk don yi musu martaba da Isa kasar ta Saudiyya.

Dama dai duk shekara haka Hukumomin kasar Saudiyya suke tarbar rukunin farko na maniyatan da suka fara Isa ƙasar domin sauke farali.

A bana dai za’a fara gudanar da aikin hajji ne a 15 ga watan Yuni a kuma kammala ibadar a Ranar 20 watan na Yuni 2014.

Ga wasu daga cikin hotunan yadda aka tarbi maniyatan

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...