Da dumi-dumi: Gwamna Yusuf ya sanya hannu kan dokar gwajin lafiyar kafin aure a Kano

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya amince tare da sanya hannu ga dokar gwajin lafiyar ga wadanda suke shirin yin aure a jihar Kano a hukumance, wadda ta tanadi duba lafiyar duk masu son aure.

Kamar yadda sabuwar dokar ta tanada, ba za a yi aure a Kano ba tare da ba da takardar shaidar lafiyar jinsin halitta, hepatitis B da C, da HIV/AIDS, da sauran cututtuka masu alaka da su.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya aikowa kadaura24, ya ce dokar tace ya zama dole a yi hakan domin rage haihuwar yara masu fama da matsalolin lafiya kamar su sikila HIV/AIDS, da ciwon hanta.

Hasashen yanayin da za’a tashi da shi gobe talata a Birnin Kano da wasu jihohin Nigeria

Wannan shiri dai ya yi daidai da kudurin gwamnan jihar Kano na inganta da samar da yanayi mai kyau ga fannin kiwon lafiya, da nufin ganin Kano ta kubuta daga matsalolin kiwon lafiya ko kuma rage radadin.

Dokar ta wajabta yin gwajin tilas na HIV/AIDS, Hepatitis, genotype, da sauran abubuwan da suka dace kafin aure.

A lokacin rattaba hannun kan dokar, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya jaddada cewa manufar aiwatar da dokar ita ce don rage yaduwar wasu cututtuka ga yaran da za’a haifa.

Dokar ta bayyana cewa duk wanda aka samu da laifin saba wa dokar, zai iya fuskantar tarar Naira dubu dari biyar, na tsawon shekaru biyar, ko kuma duka biyun.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi: Tinubu ya Iso Kano domin ta’aziyyar Dantata

Shugaban Nigeria Bola Ahmad Tinubu ya iso jihar Kano...

ALGON ta Kano Sa’adatu Soja ta sami sabon matsayi a kungiyar ALGON ta Ƙasa

Daga: Aliyu Danbala Gwarzo. Shugabar karamar hukumar Tudunwada kuma ALGON...

Da dumi-dumi: Tinubu zai zo Kano

Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu zai zo Kano ranar...

Tinubu ya sauya sunan jami’ar Maiduguri zuwa Sunan Muhd Buhari

Shugaba Bola Tinubu ya sauya sunan Jami'ar Maiduguri zuwa...